Ciwon Afendis: Abubuwa 10 da ya kamata ka sani.
- Katsina City News
- 21 Sep, 2023
- 1367
1. Afendis, wato "appendix" a turance, wani ɗan zunɓutu ne mai kamar jela a mahaɗar ƙaramin hanji da babban hanji. Girmansa ya kai girman yatsan hannu.
2. A ina afendis yake? Afendis yana nan a ciki a ƙasan cibiya kaɗan, sannan daga kwiɓin dama.
3. A likitance, afendis ba shi da wani takamaiman aiki a jiki ɗan Adam. Sai dai, wasu masanan na cewa afendis na ɗauke da wasu ƙwayoyin garkuwar jiki waɗanda ke taimaka wa jiki yaƙi da ƙwayoyin cutuka.
4. Ciwon afendis, wato "appedicitis" a turance, ciwo ne da ke kama afendis yayin da afendis ya kumbura ko kuma ya ɓule bayan ruɓewa saboda wasu dalilai.
5. Abubuwan da kan haddasa kumburin afendis sun haɗa da: harbin ƙwayoyin cuta kamar bakteriya, toshewar bakin afendis daga dunƙulallen turɓayan abinci ko bayan gida, ciwon daji/sankara, da dai sauransu.
6. Alamun ciwon afendis sun haɗa da:
- ciwo a ƙasa da cibiya, a kwiɓin dama.
- ciwo a kewayen cibiya wanda daga bisani kan zarce zuwa kwiɓin dama.
- ciwon da ke ta'azzara yayin tari ko wani yunƙuri.
- ciwo yayin da aka danna kwiɓin dama da cibiya.
- tashin zuciya da amai.
- Rashin sha'awar cin abinci.
- matsakaicin zazzaɓi, da sauransu.
7. Idan Ciwon afendis ya ta'azzara yana iya buƙatar tiyatar gaggawa domin cire shi, musamman idan ya riga ya ɓule ko kuma ana tsoron fashewarsa a kowane lokaci.
8. Barin ciwon afendis ba tare da an cire shi ta hanyar tiyata ba na da haɗarin gaske, domin ɓulewa ko fashewarsa na nufin fantsamar ƙwayoyin cuta da ke ƙunshe ciki zuwa dukan sauran kayan ciki.
9. Hanyar kariya daga ciwon afendis: babu wata sahihiyar hanyar kariya daga ciwon afendis; sai dai masana kimiyyar abinci na ganin cewa ciwon afendis bai cika kama masu cin datsar hatsi, ganyayyaki da 'yayan itatuwa ba.
Saboda haka, batun cewa afendis gidan tsakuwa ne ko kuma ciwon afendis na faruwa ne yayin da tsakuwa ta cika shi tatsuniya ce kawai!
10. Yaushe ya kamata ka ga likita? Da zarar ka fara jin wasu daga cikin alamun da aka ambata a sama, garzaya asibiti domin duba ka.
© Physiotherapy Hausa