An Tsinci Gawar Fitaccen Dan Jaridan Da Ya Bace a Zamfara
- Katsina City News
- 21 Sep, 2023
- 1500
Ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa (NUJ) reshen jihar Zamfara ta tabbatar a ranar Laraba, 20 ga watan Satumba, da kashe Alhaji Hamisu Danjibga, wakilin muryar Najeriya VON a jihar.
Jaridar Tribune ta rahoto cewa a wata sanarwa da sakataren ƙungiyar na jihar, Ibrahim Ahmad ya fitar a Gusau, ya ce an tsinci gawar marigayin ne a wani rami da waɗanda suka kashe shi suka jefa shi a ciki.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
“An gano gawar tasa ne sakamakon wani wari mara daɗi da yaran makarantar Islamiyya suka ji a bayan gidansa da yammacin ranar Laraba, 20 ga Satumba, 2023."
"Bayan an buɗe ramin, iyalansa da maƙwabta sun tabbatar da cewa gawar ta Danjibga ce."
An ruwaito Danjibga ya shafe kwanaki uku ba a san inda yake ba kafin a gano gawarsa. Majiyoyi sun ce da farko an tuntubi iyalansa su biya naira miliyan ɗaya domin a sake shi, amma waɗanda ba a san ko su wanene ba da suka halaka shi sai suka ƙara yawan kuɗin.
Rundunar ƴan sandan jihar ta cafke mutum ɗaya da ake zargi yana da hannu wajen kashe ɗan jaridan.