Tarihin Unguwar Farin Yaro Cikin Birnin Katsina
- Katsina City News
- 21 Sep, 2023
- 1762
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 21/9/2022
Farin Yaro tana yammacin tsohuwar Mayankar Katsina daga kudu ta yi iyaka da Gambarawa daga Arewa tayi iyaka da Tudun 'Yanlifidda daga gabas tayi iyaka da Malumma daga Yamma tayi iyaka da Kofar guga.
An kafa wannan unguwa shekaru da dama da suka Unguwar ta samo sunanta daga wani makeken Tafki da akayi a wajen wanda ake kira da suna "Farin Yaro" Bayanan da aka samu daga mai unguwar wurin ya nuna cewa Farin yaro Suna ne na wani aljanin ruwa da ya zauna a wurin shakaru aru-aru da suka wuce.
A zamanin da wannan tafkin ya shaharaa Katsina. A cikin tafkin akwai Kadoji daTsari da Kifaye kala-kala kowace shekara tafkin yakan cika da ruwa, ya yi Ambaliya har ma ya ci gidaje da dabbobi. Mutane sukan je kallon ruwa, da Kadoji a wurin. Gewaye da tafkin ana noman rani musamman tumatir harma mutane suka rika kiran wurin da Suna 'Tumatarawa'. A halin yanzu wannan tafki babu shi. Farin Yaro nan ne wurin da aka ba da labarin cewa:
Zamanin da wani mai gishiri ya auri wata aljana. A cikin labarin, an ruwaito cewa a zamanin da wata diyar aljannu ta rikida ta zama kyakkyawar budurwa ta tafi kasuwar Katsina da kudinta domin sayen gishiri. Duk lokacin da ta zo kasuwa da 'yan kudinta, sai masu gishiri su kore ta.
Sai wani daga Cikinsu ya kirata ya bata gishiri ba tare da ya amshi ko kwabo ba. Ita kuma duk lokacin da haka ya faru, sai ta shaida wa iyayenta, har tsawon shekara uku. Rannan sai suka ce mata ta kawo masu wanda yake yi mata wannan kyautar. Sai ta je kasuwa ta kira shi. Da ya zo sai ta fada masu cewa su fa aljannu ne, gidansu ya na nan kusa da Farin Yaro. Da suka kusa isa tafkin sai ta ce masa ya rufe idonsa, sai ya rufe, sai gashi a cikin wasu Jama 'a daban. Sai Wadannan mutanen suka ce masa mu fa aljannu ne, zaka iya Auren diyarmu? Ya ce I' ina iyawa.
Suka ce banda mata na bakin mutum, mu fa bama son daudar zina. Suka ce sun ba shi yarinyar aure, suka ce ya kawo zannuwa da kwarya goma ta goro ta goro na sa biki.
Yarinya tai masa rakiya tace ya rufe idon sai ga shi wurin gishirinsa a kasuwa.
Aka yi Aure aka sha shagali mai yawa, Ranar juma'a aka kawo amarya. A ranar makwabta suka kwana ba su yi barci ba.
Da ango ya shiga dakin amarya. sai ya ji wani Irin kamshi. Daki ya haske kamar rana. Ga gadaje da shinfidu nan iri-iri kamar gadon Sarki Mutumen nan ya zama mai kudi a garin Katsina. Ya zama ma'abucin labarin duniya. Amma fa da ya rasu ba a sami kome ba a gidansa. Aka yi ta al'ajabi da wannan al'amari. Wannan labarin wasu mutane sun dauke shi a matsayin al'mara, wasu kuma na ganin gaskiya ne.
Daga cikin abubuwan tarihi da aka yi a Farin Yaro akwai Kuka mai kaikainu. Ita wannan Kuka an yi ta ne kudu maso gabas da tafkin farin yaro. Bayanan da aka samu Sun nuna cewa babu wani mahalukin da ke iya zuwa gindin wannan kuka da rana tsaka ko kuma a cikin dare. A halin yanzu wannan Kuka babu ita.
An kafa makarantar firamare a Farin Yaro a cikin shekara miladiyya 1962. Tsohuwar Yan E ta Katsina ce ta gina ta. Makarantar ta yaye dalibai da yawa kuma wannnan makarantar tana daga cikin manyan makarantun firamare na Karamar Hukumar Katsina.
Mun ciro daga Littafin Tarihin Unguwannin Birnin Katsina da kewaye wanda Hukumar Binciken Tarihi da kyautata Al'adu ta jihar Katsina ta Wallafa.