Muhammad Ali Hafizy | Katsina Times.

Dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Katsina, Hon. Sani Aliyu Danlami ya jagoranci kaddamar da aikin hanyoyi a wasu daga cikin unguwannin dake cikin karamar hukumar.
Unguwannin wadanda suke fama da matsalolin hanyar zirga-zirga wadda take jawo cinkosu da kuma caɓewa a lokutan damuwa sun hada da Kadarko, Modoji, da kuma Gidan Dikko Ladan.
Za a dauko titin daga unguwar Kadarko zuwa Mariamoh Jari Road, sai kuma daga unguwar Modoji (G.R.A) zuwa gidan Sarkin Dawaki, sannan kuma daga unguwar Modoji (G.R.A) gidan Dikko Ladan zuwa Express way.
A jawabin shi wajen taron Hon. Danlami ya bayyana ma mahalarta taron cewa aikin ba zai dauki wasu lokuta ba wajen kammalawa, ya bayyana cewa za'a gudanar da aikin cikin wata guda kacal, ba tare da bata lokaci ba.
"Ina tabbatar da al'umma cewa inshallah wannan aikin ba zai dauki lokaci ba za'a kammala shi cikin wata guda mai zuwa inshallah" ya kara da cewa"Nan da sati Uku mai zuwa duk wani wanda zai hau titin to zai tabbatar da cewa ana dab da kammala aikin koma ace an kammala" inji shi.
Ya kara da cewa zaya kara dagewa wajen samar ma al'ummar karamar hukumar Katsina abubuwan amfanuwa tun daga kan samar ma matasa ayyukan yi, samar da walwala ga manoma, samar da hanyoyi da kuma fitilu masu amfani da hasken rana.
"Zamu yi kokari wajen ganin mun sauke nauyin da ya rataya a kanmu. A lokacin da na hau wannan kujerar cikin ikon Allah nayi rijiyoyi guda 118, na sanya fitilu masu amfani da hasken rana guda 560, nayi sola mai amfani da hasken rana guda 9, na gina azuzuwa guda 18". In ji shi.
Taron ya gudana a unguwar Kadarko cikin garin Katsina a ranar Asabar 19 ga watan Yuli 2025, tare da samun halartar manyan baki da dama.