Garuruwa Biyar a Kankia na Ƙarkashin Barazanar Ƴan Bindiga – Al’umma na Neman Taimako

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes19072025_105029_FB_IMG_1752922016107.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | KatsinaTimes

Akalla garuruwa biyar da ke kudancin yankin Tafashiya a ƙaramar hukumar Kankia ta jihar Katsina na fama da munanan hare-haren ƴan bindiga masu garkuwa da mutane, lamarin da ke tilasta wa mazauna yankunan barin gidajensu domin neman mafaka a wasu sassa.

Garuruwan da lamarin ya fi tsananta sun haɗa da Barkawa, Ƴar Santa, Badole, Doza da Jakiri, inda sama da mutane 3,000 ke zaune suna dogaro da noma da sana'o'in hannu. Sai dai yanzu rayuwar al’umma ta shiga cikin rudani saboda tasirin harin ƴan bindiga da ya katse duk wata rayuwa ta yau da kullum.

Rahotanni sun nuna cewa a cikin kwanaki huɗu da suka gabata, ƴan bindiga sun kai hari a yankin inda suka kashe mutane huɗu tare da jikkata wasu da dama.

“Babu jami’an tsaro ko ƴan sa kai a nan, muna rayuwa ne kamar dabbobi a daji. Kowanne lokaci ana iya kawo mana hari. Mutane da dama sun tsere sun bar gidajensu,” inji wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa.

Wani dan asalin yankin da yanzu ke zaune a garin Malumfashi, Nasiru Salisu, ya shaida wa KatsinaTimes cewa gidansa ya zama mafakar 'yan gudun hijira, mata fiye da goma sha biyar da suka tsere daga yankunan da aka fi kai farmaki.

“Ina da gidaje a Malumfashi inda waɗannan mata da yara suka sauka. Kuma ba su kaɗai ba ne, wasu sun tsere zuwa wasu sassa dabam-dabam na ƙasa bisa la’akari da inda za su samu sauƙin rayuwa,” inji shi.

Ya ce lamarin ya kai wani matsayi da ke bukatar gaggawar daukar mataki daga gwamnati da hukumomin tsaro.

“Damina ta kama, amma babu wanda ke iya shiga gona. Makarantu sun daina aiki balle cibiyoyin lafiya,” inji wani da ya tsere daga yankin.

Al’umma na roƙon gwamnati da hukumomin tsaro da su hanzarta kawo ɗauki ta fannin tsaro da agajin jin ƙai ga waɗanda rikicin ya rutsa da su.

Follow Us