NA ZIYARCI KABARIN ANNABI SALIHU (As) DA ANNABI HUDU(AS).
- Katsina City News
- 20 Sep, 2023
- 2831
@ katsina times
@ jaridar taskar labarai
Birnin Najaf yana kilomita 178 daga Babban birnin Baghdad na kasar Iraq.
A Najaf akwai wata Makabarta da ake Kira Wadis Salam. Hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta UNESCO ta ayyana makabartar a mafi girma da tsohon Tarihi a Duniya.
Kundin adana bayanai na wikipedia sun ce makabartar nada fadin hekta miliyan daya da dubu dari hudu da tamanin da bakwai da doriya.
A makabartar akwai kaburburan sahabai, waliyai, manyan Masana addinin musulunci.
A makabartar a kwai kabarin Annabi salihu(as) da kuma Annabi Hudu(as).
Na ziyarci makabartar na kuma ZIYARCI KABARIN Annabi salihu(as) da kuma Annabi Hudu(as).