UMYU Ta Rantsar Da Sabbin Daliban Ilimi mai Zurfi, Da Jaddada Kudirinta na Inganta Ilimi

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes15052025_171400_FB_IMG_1747329123642.jpg


Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Time

Jami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU) da ke Katsina ta gudanar da taron maraba da sabbin ɗaliban digiri akan ilimi mai zurfi (postgraduate) da aka rantsar cikin jami’ar a bana, a wani taro mai cike da nishadi da aka gudanar a dakin taro na jami’ar.

Mataimakin Shugaban Jami’a na ɓangaren harkokin gudanarwa, Farfesa Aliyu Mukhtar, wanda ya wakilci Shugaban Jami’ar, Farfesa Salihu Shehu Muhammad, shi ne ya gabatar da jawabin maraba ga sabbin ɗaliban.

A cikin jawabin nasa, Farfesa Mukhtar ya taya sabbin ɗaliban murna bisa samun nasarar shiga wannan babbar jami’a, yana mai bayyana hakan a matsayin alamar ƙwarewa, jajircewa, da kuma niyyarsu ta zurfafa bincike da neman ilimi.

“Samun ku a nan jami’ar ba wai kawai ya dogara ne da nasarorin da kuka samu a baya ba, har ila yau muna da yakinin cewa za ku bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen samar da ilimi da cigaban kasa,” in ji shi.

Farfesa Mukhtar ya bayyana cewa neman digiri na biyu ba kawai tafiya ce ta ilimi ba, har ila yau wani babban alƙawari ne na gudanar da bincike mai zaman kansa, tunani mai zurfi da kuma bayar da gudunmawa ga al’umma ta hanyar ilimi.

“A UMYU, mun kuduri aniyar samar da muhalli mai inganci, mai ɗauke da kayayyakin more rayuwa, jagoranci daga masana, da duk wata gudunmawa da kuke buƙata domin cin nasara,” in ji shi.

Ya jaddada cewa sabbin ɗaliban za su shiga cikin bincike mai tushe su bayar da gudunmawa ga tattaunawar ilimi, tare da kiyaye kyawawan ɗabi’u da ƙa’idojin bincike da gaskiya.

“Dole ne ku kasance masu kima, gaskiya da himma. Abin da kuke yi zai bayyana ba kawai a kanku ba, har da wannan babbar cibiyar ilimi,” in ji shi.

Ya kuma bukaci ɗaliban da su amfana da damammakin da jami’ar ke bayarwa, ciki har da tarukan bita, haɗin gwiwar fannoni daban-daban da tarukan masana da ake gudanarwa a jami’ar.

A ƙarshe, Farfesa Mukhtar ya jaddada kudirin jami’ar na tabbatar da nasarar karatun ɗalibai, yana mai cewa jami’ar na da yakinin za su kawo canji mai ma’ana a lokacin zamansu a jami’ar da kuma bayan kammala karatu.

“Muna sake taya ku murna, kuma muna maraba da ku zuwa Jami’ar Umaru Musa Yar’adua,” in ji shi.

Taron ya kasance daya daga cikin muhimman abubuwan da ke nuna shirye-shiryen jami’ar wajen tallafa wa sabbin daliban digiri na biyu domin samun gogewa da kwarewa a fagen bincike da ilimi.

Follow Us