Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai ta fara bita kan yadda ta gudanar da ayyukan ta a zangon aiki na biyu, domin tabbatar da cika manyan abubuwan da Shugaban Ƙasa ya ɗora mata ta hannun Ofishin Tsare-tsare da Bibiyar Ayyuka (CDCU) da ke Ofishin Shugaban Ƙasa.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya jagoranci zaman bitar da aka gudanar a Abuja ranar Talata, inda ya bayyana cewa taron yana da nasaba da yarjejeniyar aiki da ya rattaba hannu a kai da shugabannin hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar a watan Agustan 2024.
Ya ce kafin hakan ma, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniya da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan manyan abubuwan da ma’aikatar za ta cimma.
A cewar sa, wannan bita tana da nufin tantance yadda aka samu cigaba a aiki, da kuma tabbatar da cewa hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar suna tafiya daidai da abin da aka ɗora masu a matsayin nauyi.
Ya ce: “Muna nan ne don sauraron shugabannin hukumomi domin mu ga yadda suka aiwatar da muhimman abubuwan da muka rattaba hannu a kai. Idan akwai ƙalubale, za mu tattauna su. Idan akwai cikas, za mu duba abin da za mu iya yi domin shawo kansu.”
Ministan ya bayyana wannan taro a matsayin hanyar tantance kai kafin a kai tsakiyar wa’adin gwamnatin yanzu.
Ya ce: “Ku tuna cewa wannan gwamnati ta fara aiki kusan shekaru biyu da suka gabata. Cikin ƙasa da wata guda daga yanzu, wannan gwamnati za ta kai rabin wa’adin ta a ranar 29 ga Mayu.
"Saboda haka, lokaci ya yi – kamar yadda Ofishin Shugaban Ƙasa ya nema – da kowace ma’aikata za ta fidda sakamakon aikin ta kan abubuwan da ta tsara kuma aka amince da su ta hannun ofishin CDCU da ke Ofishin Shugaban Ƙasa."
Idris ya kuma jaddada cewa ma’aikatar sa na jajircewa wajen samar wa ‘yan Nijeriya da sahihan bayanai game da nasarorin gwamnati da kuma ƙalubalen da take fuskanta.
Ya ce: "Abin da wannan ma’aikatar ke yi shi ne tabbatar da cewa ba wai kawai muna wayar da kan ‘yan Nijeriya kan abubuwan da ke cikin hangen nesa na Shugaban Ƙasa ba, har ma muna bayyana ƙalubalen da ke akwai cikin gaskiya da riƙon amana? Tabbas, wannan ne abin da muka ɗauka tun farko kuma za mu ci gaba da bin wannan hanya.”
Ya ƙara da cewa babban aikin ma’aikatar shi ne tsarawa da aiwatar da dabarun sadarwa masu ma’ana domin inganta gaskiya da rarraba bayanai game da manufofi da shirye-shiryen gwamnati, yaƙi da yaɗa ƙarya, da kuma ƙarfafa wayar da kan 'yan ƙasa bisa fifikon gwamnatin Tinubu.
Taron ya samu halartar shugabannin hukumomi kamar haka: Darakta Janar na Hukumar Talabijin ta Nijeriya (NTA), Kwamared Abdulhamid Dembos; Darakta Janar na Hukumar Rediyon Tarayyar Nijeriya (FRCN), Dakta Mohammed Bulama; Darakta Janar na Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), Mista Lanre Issa Onilu; Darakta Janar na Hukumar Kula da Gidajen Rediyo da Talbijin ta Ƙasa (NBC), Mista Charles Ebuebu; Darakta Janar na Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace; Darakta Janar na Hukumar Kula da Tallace-tallace (ARCON), Dakta Olalekan Fadolapo; da Manajan Darakta na Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), Malam Ali M. Ali.