KAR A SA GWAGWARE FOUNDATION CIKIN TSEGUMIN SIYASA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes04052025_094455_Screenshot_20250504-104343.jpg

Daga Muhammad Ɗanjuma 

@ Katsina times 

Na ga wata takardar ƙorafi da wasu mutane uku suka rubuta ta koke a kan mataimakin shugaban jam'iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Bala Abu Musawa.

Masu ƙorafin suna da 'yancin rubuta takardar, suna kuma da 'yancin bin kokensu, domin su ma 'yan ƙasa ne, 'yan jiha, kuma 'yan jam'iyyar APC ne, kuma suna ganin abun da suke koke a kansa suna tabbacin an yi masu kuskure.
 
Amma inda suka ɓata rawarsu da tsalle shi ne, amfani da Gidauniyar Gwagware, wadda Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya kafa.

A gabana aka ƙaddamar da Gidauniyar a ɗakin taro na Hukumar kula da ma'aikatan ƙananan hukumomi na jihar Katsina. 

A wajen ƙaddamar da Gidauniyar a lokacin Malam Dikko Raɗɗa ya ce Gidauniyar ce ta tallafi da taimakon al'umma. Ya ce wasu ayyukan da muke ne muka ga ya kamata mu mayar na alheri muka ga ya kamata mu mayar da su a tsare. Ya ce ba ƙungiyar siyasa ba ce.

Duk jawaban da aka yi a taron har da wanda Gwamnan Katsina na lokacin, Alhaji Aminu Bello Masari ya yi, sun jadadda cewa Gidauniyar ta zama mai zaman kanta don taimakon al'umma.

Ba ni da mukami a Gidauniyar, amma daga kafa ta zuwa lokacin da aka shiga harkar neman takara na fi kowa tallata ayyukan Gidauniyar.

Duk fitar da za a yi kai gudummuwa inda wani ibtilai ya faru, ni ke tafiya da 'yan jarida, kuma jawabin da Malam Dikko kan yi in mun je shi ne Gidauniyar tallafa wa al'umma ce, ba ta siyasa ba.

Duk shekara taron da Gwagware kan yi na tallafin Azumi, kafin a samu tikitin takara, ana gama taron ni zan jagoranci 'yan jarida zuwa gidan Gwagware a Ɓatagarawa ya yi ƙarin haske a kan wannan aikin alheri da ya assasa.

Ina da wani tsohon bidiyo da na taɓa yi masa tambaya a gidansa na Ɓatagarawa cewa ko wata rana in zai yi takara zai amfani da Gidauniyar?

Sai ya ban amsa kamar haka. "Duk ɗan siyasa da ya ce maka takara ba ta jininsa, to bai cancanta ba ne. Mulki kuma na Allah ne."

Ya ce, "Amma Gidauniyar Gwagware don ayyukan alheri aka kafa ta, kuma za ta ci gaba in Allah ya yarda har jikoki."

Lokacin Malam Dikko Raɗɗa yana SMEDAN, in na shiga Abuja nakan je wajensa. In har na samu ganin shi mukan tattauna abubuwa da yawa, daga cikin su har da ƙarfafa gwaiwar ayyukan alheri na Gidauniyar Gwagware.

Gidauniyar Gwagware ba Kwankwasiya ba ce, wadda ta ginu a kan aƙida siyasa, kamar yadda na fahimta a tsawon hulda ta da jagoranta da kuma ayyukan da suka riƙa yi ina biye da su.

Kuma wannan kambin ya kamata su riƙe su ci gaba da shi.

Darrusa a ƙasa da jihohi ya nuna duk ayyukan alheri da aka danganta da siyasar mai mulkin da ke sama suna mutuwa da barinsa bisa madafun iko.

A Abuja an kafa 'Yar'adua Center sakamakon waɗanda suka kafa ta tun farko a 2000, sun nisanta ta da waɗanda ke kan karagar mulki, duk da kuwa da cewa a lokacin shugaban ƙasa da mataimakinsa na lokacin sune suka kafa Cibiyar (Obasanjo da Atiku).

A 2000 Marigayi MD Yusufu ya kafa wurin horas da matasa sai na sanya wa wurin MD Yusufu Vocational Centre yana gani ya ce, "Cire sunana. Ina siyasa. Ana iya danganta wajen da siyasa ta da takarar da nake yi ta neman shugaban ƙasa."

Mun cire mun kuma nisanta wajen da kowace siyasa har yanzu 2025 Cibiyar na taka rawa a Katsina. 

Gwagware Foundation na iya neman alfarmar ƙuri'a ga al'umma lokacin zaɓe, ana iya ba 'ya'yanta muƙamai don su ma 'yan jiha ne.

Amma shiga tsegumin siyasa, wannan kuskure ne. 

A lokacin tsohon Gwamnan Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema, an yi ƙungiya mai suna Shema Partnership, waɗanda suka riƙa tallata ayyukan Shema da ba shi kariya. 

Haka ma a lokacin Masari, an yi Masari Restoration, waɗanda suka riƙa wannan aikin.

Yanzu ma ana iya samun wata ƙungiya mai wani suna don wannan aikin, amma ba Gwagware Foundation ba.

Wannan kuma ra'ayina ne, kuma ra'ayi riga, kowa da irin tasa.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com 
Jaridar taskar labarai 
@ www.taskarlabarai.com 
07043777779 08057777769.
Email.newsthelinks@gmail.com

Follow Us