Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
A ranar Litinin, 14 ga Afrilu, 2025, an gudanar da bikin rantsar da sabbin shugabannin kananan hukumomi guda 34 na jihar Katsina a babban filin wasa na Muhammadu Dikko da ke birnin Katsina. Dukkanin shugabannin da aka rantsar sun fito ne daga jam’iyyar APC mai mulki, wadda ta samu nasarar lashe kujerun a zabukan da suka gabata.
Bikin ya kasance mai armashi tare da halartar shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje da manyan jiga-jigan ‘yan siyasa daga ciki da wajen jihar, tsofaffin shugabanni da masu ruwa da tsaki a harkar mulki. An gabatar da kowane sabon shugaba tare da hotonsa da sunansa, inda aka nuna alfahari da yadda zabukan suka gudana cikin kwanciyar hankali.
Jim kaɗan bayan kammala rantsarwar, Gwamnatin jihar Katsina ta ofishin sakataren ta na Jiha, ta sanar da naɗin Alhaji Lawal Rufa’i Safana a matsayin shugaban sashin sa-ido akan ayyukan kananan hukumomi tare da bashi matsayi na mai ba gwamna shawara ta musamman a fannin mulkin kananan hukumomi.
Gwamna Radda ya bayyana cewa naɗin Alhaji Lawal Rufa’i Safana ya biyo bayan kwarewarsa da dogon tarihi a harkar mulkin kananan hukumomi, wanda hakan zai ba da gudunmuwa wajen tabbatar da nagartaccen shugabanci a wannan mataki na mulki da ke da matukar muhimmanci ga rayuwar jama’a.
A jawabinsa yayin bikin, Gwamna Radda ya jaddada muhimmancin shugabanci nagari da gudanar da mulki ba tare da nuna bambancin jam’iyya ba. Ya ce:
“Yanzu kun zama shugabannin al’umma gaba ɗaya, ba na jam’iyya kawai ba. Don haka, ku tabbatar da cewa kun jawo al’umma a jikinku, ku saurari bukatunsu, ku kuma yi aiki domin kawo ci gaba da zaman lafiya a kananan hukumomin da kuke jagoranta.”
Ya kuma gargade su da su nisanci cin hanci da rashawa tare da mayar da hankali wajen cika alkawurran da suka dauka lokacin yakin neman zabe.
Jerin Sabbin Shugabannin Kananan Hukumomi 34 a Jihar Katsina
1. Bakori LG: Aminu Dan Hamidu
2. Batagarawa LG: Yahaya Lawal Kawo
3. Batsari LG: Manir Ma’azu Ruma
4. Baure LG: Saminu Sulaiman Baure
5. Bindawa LG: Badaru Musa Giremawa
6. Charanchi LG: Ibrahim Sani Koda
7. Dandume LG: Bashir Sabiu Gyazama
8. Danja LG: Rabo Tambaya
9. Danmusa LG: Ibrahim Namama
10. Daura LG: Bala Musa
11. Dutsi LG: Abdurazak Adamu
12. Dutsinma LG: Abdulsalam Shema
13. Faskari LG: Sirajo Aliyu Daudawa
14. Funtua LG: Abdullahi Goya
15. Ingawa LG: Abdullahi Idris
16. Jibiya LG: Sirajo Ado Jibiya
17. Kafur LG: Haji Sirajo Bature
18. Kaita LG: Engr. Bello Lawal 'Yandaki
19. Kankara LG: Kasimu Dantsoho Katoge
20. Kankia LG: Lawal Abdullahi
21. Katsina LG: Isah Miqidad AD Saude
22. Kurfi LG: Babangida Abdullahi
23. Kusada LG: Sani Aminu Dangamau
24. Mai’adua LG: Salisu Mamman Na Allahu
25. Malumfashi LG: Muntari Abdullahi
26. Mani LG: Dr. Inusa Muhammad Sani
27. Mashi LG: Salisu Kalla Dankada
28. Matazu LG: Shamsu Muhammad Sayaya
29. Musawa LG: Aliyu Idris Gin-Gin
30. Rimi LG: Muhammad Ali Dan Rimi
31. Sabuwa LG: Engr. Sagiru Tanimu
32. Safana LG: Abdullahi Safana
33. Sandamu LG: Usman Nalado Matawalle
34. Zango LG: Babangida Yardaje
Katsina Times na ci gaba da bibiyar matakan da sabbin shugabannin da naɗaɗɗen shugaban sa-ido za su dauka domin inganta shugabanci da kawo sauyi a matakin kananan hukumomi a fadin jihar.
Za a iya samun karin hotuna da bidiyo na bikin rantsarwar a shafukanmu na sada zumunta da gidan yanar gizo.