Najeriya Ta Jaddada Kudirin Karfafa Dangantakar Ta da China

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes13042025_183016_FB_IMG_1744568807373.jpg


Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Yusuf Tuggar, ya sake jaddada aniyar Najeriya na zurfafa dangantakar da ke tsakanin ta da Jama’ar China, musamman a manyan fannoni da ke da nasaba da ci gaban tattalin arziki da diflomasiyya.

Ambasada Tuggar ya karɓi bakuncin Hu Chunhua, Mataimakin Shugaban Taron Tattaunawar Siyasa na kasar China, a Abuja, inda suka tattauna kan sabunta dabarun hadin gwiwa da karfafa zumunta tsakanin kasashen biyu.

Dangantakar Najeriya da China wadda ta shafe fiye da shekaru hamsin na ci gaba da habaka, inda China ta kasance daya daga cikin manyan abokan kasuwanci na Najeriya. A shekarun baya-bayan nan, darajar cinikayyar da ke tsakanin kasashen biyu ta kai sama da dala biliyan 12.

China na taka muhimmiyar rawa a ci gaban Najeriya ta fuskar saka hannun jari a fannonin gine-gine, makamashi, fasahar zamani da kuma noma wanda ke taimaka wa tattalin arzikin Najeriya ya habaka.

A yayin ganawar, Ambasada Tuggar ya jaddada bukatar ci gaba da karfafa hadin kai da kuma gano sabbin damammaki da za su amfanar da bangarorin biyu. Ya ce, “Wajibi ne mu ci gaba da gina kyakkyawar alaka mai amfani da girmama juna wadda za ta haifar da ci gaba mai dorewa ga kasashenmu.”

Taron ya kuma nuna karfin zumunci da fahimtar juna da ke tsakanin Najeriya wacce ke da tattalin arziki mafi girma a Afirka da China, wacce ke matsayi na biyu a duniya ta fuskar karfin tattalin arziki.

Follow Us