UNICEF da Gwamnatin Jihar Katsina Sun Sanya Hannu Kan Sabuwar Yarjejeniyar Aiki Don Inganta Rayuwar Yara

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes10042025_202058_FB_IMG_1744315487610.jpg



Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times

A wata sabuwar alaka da ke nuna ci gaba da hadin gwiwa, Hukumar Kula da Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) da Gwamnatin Jihar Katsina sun rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar aiki ta tsawon shekaru uku a ranar Alhamis, 10 ga Afrilu, 2025 domin inganta rayuwar yara da mata a fadin jihar.

Da yake wakiltar shugaban UNICEF a Najeriya, Rahama Rihood Mohammed Farah, jami’in kula da lafiyar jama’a a ofishin UNICEF na Kano, Dr. Sereke Seyoum Deres, ya bayyana cewa sabon tsarin ya kunshi hanyoyi daban-daban da za su taimaka wajen bunkasa fannin lafiya, abinci mai gina jiki, ilimi, tsaftar muhalli, kare hakkin yara da kuma taimaka wa marasa galihu.

Dr. Sereke ya yabawa Gwamnatin Jihar Katsina a karkashin jagorancin Gwamna Malam Dikko Umar Radda bisa goyon baya da hadin kai da take bai wa shirye-shiryen UNICEF, musamman a fannonin da suka shafi kiwon lafiya da jin dadin yara da mata. Ya ce, “Wannan tsarin aiki ba kawai a takarda ba ce, alamar burin hadin gwiwarmu ce domin samar da rayuwa mai inganci ga kowane yaro a Jihar Katsina.”

Ya bukaci gwamnati da ta kara zuba jari daga cikin albarkatunta na cikin gida a bangarorin kiwon lafiya, abinci mai gina jiki, tsaftar muhalli da kare yara domin rage dogaro da tallafin kasashen waje, tare da yabawa tsarin HADACA MSH da aka kirkira a fannin lafiya a matsayin abin koyi.

Ya kara da cewa dole ne a ci gaba da yaki da cutar shan inna (polio) tare da tabbatar da cewa kowanne yaro ya samu rigakafi, inda ya bukaci gwamnati da shugabannin al’umma da na addini da su dauki matakin yakar masu kin amincewa da rigakafi.

A nasa jawabin, Gwamna Dikko Umar Radda ya bayyana cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali sosai kan bangaren ilimi da lafiya, inda ya ce an kashe sama da naira biliyan 120 wajen gina da gyaran makarantu sama da 500, da horar da malamai, da samar da tallafi da guraben karatu ga dalibai da matasa.

Dangane da fannin lafiya kuwa, Gwamna Radda ya ce jihar ta karbi kayayyakin aikin jinya daga kungiyoyin World Medical Relief da Project Bio na Amurka, ciki har da na’urorin MRI da CT scan, tare da bullo da tsarin adana bayanan lafiya na zamani (EHR), da kuma saka na’urorin tantance halartar ma’aikata a cibiyoyin kiwon lafiya.

Haka kuma, an gyara fiye da cibiyoyin lafiya na matakin farko 150 tare da samar da ruwan sha, wutar lantarki ta hasken rana, da motocin ambulan masu kafa uku (tricycle). Jihar ta kuma raba babura 361 domin aikin rigakafi a fadin jihar tare da hadin gwiwar UNICEF da GAVI.

Gwamna Radda ya tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da bayar da goyon baya da hadin kai wajen tabbatar da nasarar aiwatar da wannan sabon tsarin, yana mai cewa, “Wannan aikin namu ne, ba taimako bane. Kuma hanya mafi kyau ta nuna godiya ita ce mu tabbatar da nasararsa.”

A karshe, UNICEF ta sake jaddada kudirinta na ci gaba da tallafa wa Gwamnatin Jihar Katsina domin tabbatar da cewa kowanne yaro ya samu damar rayuwa mai inganci da cika hakkinsa.

Follow Us