Kungiyar Dikko Project Movement Ta Kai Ziyarar Ta'aziyya Ga Uwargidan Gwamnan Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes04042025_071511_IMG-20250404-WA0090.jpg

Katsina Times 

Shugaban kungiyar Dikko Project Movement, Hon. Musa Yusuf Gafai, tare da wasu jiga-jigai na kungiyar, sun kai ziyarar ta'aziyya ga Uwargidan Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Zulaihat Dikko Radda, a fadar gwamnatin jihar, biyo bayan rasuwar mahaifiyar Gwamna, Hajiya Safara’u Umar Bare-bari.

A yayin ziyarar, Hon. Musa Gafai ya bayyana cewa rasuwar Hajiya Safara’u babban rashi ne ba kawai ga Gwamna Malam Dikko Radda da iyalansa ba, har ma ga daukacin al’ummar musulmi. Ya kara da cewa irin tarbiyyar da marigayiyar ta bayar a rayuwarta ta haifar da manyan 'ya'ya masu kishin al'umma.

Shugaban kungiyar da tawagarsa sun gudanar da addu’o’i na musamman domin neman gafara da rahamar Allah ga marigayiyar, tare da fatan Allah ya sanya Aljanna ce makomarta.

A nata bangaren, Uwargidan Gwamnan Jihar Katsina, Hajiya Zulaihat Dikko Radda, ta nuna godiya da farin cikinta bisa wannan ziyara, inda ta ce irin wannan goyon baya na daga cikin abubuwan da ke karfafa gwiwar iyalai a lokacin jimami.

Ziyarar ta'aziyyar ta gudana cikin yanayi na tausayi da addu'o'in alheri.

Follow Us