Daga Ɗanjuma Katsina @ Katsina times
Wasa-wasa an ɗau shekaru ana fama da matsalar 'yan bindiga, dabbobi jahilai marasa imani. Matsalar kuma babu ranar ƙarewarta nan kusa.
Kullum sai mafarki da tsammanin iska da tunanin doki zai tashi sama kamar shawo.
Kullum sai jiran gawon shanu da jiran tsuntsu daga sama gasasshe.
Kullum sai yaudarar kai da yaudarar hankali da zaluntar basirar da Allah ya yi mana ta cewa wai zai a yi sulhu tsakanin kare da ɗanyen nama.
Lokaci ya yi da ya kamata mu farka da fara nazarin ya za mu zama soja zallarmu domin kare kanmu da mutuncinmu.
Lokaci ya yi da za mu fara tunanin da rayuwa cikin ƙasƙanci gwara mutuwa cikin izza da daraja.
Lokaci ya yi da Musulmi ya kamata su fara sanin akwai wata kyauta da Allah ya yi masu mai sunan mutuwar shahada, wadda Musulunci ya fayyace yadda take, kuma ya ake samun ta.
Lokaci ya yi da za mu fara tunanin shin haka za mu yi ta rayuwa cikin firgici da tsoron yau ɗan'uwanka ne na jini ko na addini ko ko na 'yan adamtaka aka mai da shi tamkar dabba?
Lokaci ya yi da za mu fara fuskantar gaskiya da nazarin kalaman mutanen da zan kawo misalin guda uku kacal, amma waɗanda suka yi su suna da yawa.
1, Tsohon Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari ya taɓa faɗi lokacin yana Gwamna cewa, dole mutane sai sun tashi sun kare kansu da kansu kafin a iya maganin 'yan bindiga.
Cikin damuwa ya ce, ko gwafa ka riƙe, ko cizo ka yi, ko da haka ne kawai za mu 'yantar da kanmu.
Ya ce gwamnatin tarayya ko jiha ba ta da jami'an tsaron da za ta iya kare kowa.
Ya ba da misali da wata ƙaramar hukuma mai al'umma sama da dubu 400, amma 'yan sandan da ke cikin ta su 37 ne kacal.
Wannan kira har Masari ya bar mulki yana yawan yin sa, amma ba a saurare shi ba, ba a ɗau matakin da ya dace ba.
Ya bar mulkin yanzu Abuja-Kaduna yake zaune, duk inda za shi a jirgin sama ko a cikin kwambar jami'an tsaro. Yana mulkin ya faɗi gaskiyar halin da ya sani. Kuma a nan ɓangaren ya fita. Yanzu wa ke wahala?
Shugaban sashen tsaro na leƙen asiri ko tattara bayanan sirri, mai suna Osita a wani jawabin da ya yi a Abuja, wanda yana nan a shafukan jaridun Katsina Times yake faɗin cewa, ƙasar nan ba ta da isassun jami'an tsaron da za ta iya kare kowa a kowane yanayi, dole mutane sai sun riƙa kare kansu da kansu.
Ya ce maharan nan mutane ne, suna son su rayu. In suka san za su iske turjiya da martani ba su kai hari a gari.
A jawabin nasa har ya ba da wasu misalai.
3, Tsohon shugaban soja ƙasa na Nijeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai, cewa ya yi, ko dai jama'a su ɗau matakin kare kansu kafin gudunmuwar soja, ko kuma yaƙin nan a kwashe shekaru 100 ana yin sa.
KARE KAI A WASU KASASHEN
Tarihi ya tabbatar da in matsalar tsaro ta yi muni ta cikin gida ko ta yaƙi ko da kuwa na basasa ne, matakin kowa ya kare kansa, kowa ya zama sojan kansa, wannan shi ne kan tsaida lamarin.
Lokacin yaƙin duniya II da ƙasashen Turai suka ga Adolf Hitler na neman cin su da yaƙi, horas da mutane suka yi, matakan kare kansu da kuma yaƙin sunƙuru ga sojan Hitler.
Littafin da Firaministan Birtaniya na lokacin, Winston Churchilll ya wallafa, ya bayyana cewa nasarar farko da suka samu ita ce ta jama'a sun zama sojojin kansu.
Shi ma Hitler a littafin da ya rubuta na tarihin rayuwarsa mai suna MEIN KAMPF cewa ya yi, kowa a ƙasar Jamus ya zama soja da shirin ko-ta-kwana.
A lokacin yaƙin basasa na Biafara, sojan Nijeriya na fagen daga, amma wasu mutane ƙarƙashin jogarancin tsohon Sufeto-Janar na 'yan sandan Nijeriya, Malam MD Yusufu ɗan Katsina da Malam Lamiɗo Sanusi mahaifin Sarkin Kano Sanusu Lamiɗo Sanusi, suna bin garuruwan da sojan Biafara suka yi tunga suna nuna masu yadda za su kare kansu da kuma yi wa 'yan tawayen Biafara zagon ƙasa, kamar yadda yake a rubutun sirri wanda aka taskace na tarihi. Tsarin sun ba shi sunan Civil Defence Corps.
Gwagwarmayar da waɗannan fafaren hula suka yi ita ta ba da nasarar yaƙin da haɗewar Nijeriya a matsayin ƙasa ɗaya.
A littafin da kakakin Biafara, Uche Chukwumerije ya rubuta, littafin ana aikin buga shi ya rasu.
A cikin littafin ya faɗa cewa ba ƙarfin soja Nijeriya ba ne ya kai su ƙasa, amma akwai tasirin aikin Civil Defence Corps.
Ƙasar Amurka ita ce ƙasar da ake kira mafi cigaba a duniya da ayyukan ɓata-gari ya yi ƙamari, sama da shekaru 40 suka amince da mallakar bindiga da koyon harbi da kuma 'yancin kare kai.
A shekarar 2023 ana hira da mataimakiyar shugabar Amurka ta lokacin, Madam Kamala Harris a tattaunawa ta talabijin da ake kira OPERA, aka ce mata in wani ya yi kutse ya faɗo maki gida ya za ki yi da shi? Gaban talabijin sama da mutane miliyan 100 na kallon ta ce, "Harbe shi zan yi."
Ta ƙare da cewa 'yancin ƙasar Amurka ya ba ta wannan damar.
Harris duk rayuwarta Lauya ce, kuma mai gabatar da waɗanda ake zargi da aikata laifuffuka a gaban kotu.
Lokacin da za mu fuskanci sulhu da ake tsammani a ƙarƙashin ƙasƙanci mafarki ne, kuma mummuna.
'Yan bindigar nan suna da makamai da yawa a hannunsu, suna da ƙasa, wato daji inda suka ɗauka sansaninsu, suna samun kuɗi da ta'addacin, suna jin iko, kuma sun shimfiɗa ikon nasu.
Ga jahilicin addini, jahilcin ilmin zamani, jahilcin wayewa, ba tarbiyyar ruhi, ba wani aiki ko kaɗan da zai ba zuciyarsu ɗigo na imani, ga dabbaci da ta'addaci, ga ƙwaya da kullum suke rayuwa a cikin shanta. Babu wani hadafi tare da su. A haka za a zauna da su a yi sulhu?
Daga darussan da muka koya a baya da kuma wanda ya faru a wasu garuruwa da jihohi, ba inda sulhun da aka yi da 'yan ta'adda ya ba da natija. Kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu.
Mafi muni matasansu da yara ƙanana da ke a dajin sun rungumi wannan ta'asar tana burge su, suna jin daɗinta. Duk abin da yara da matasa suka runguma, wahalar bari ke gare shi.
Duk wani zaman sulhu, lokaci suke ƙara saye da kuma ƙara tsare-tsare da sayen abinci da biyan wata buƙatarsu, amma in ka cire wannan Shafa Labari Shuni ne. Ta zo mu ji ta ne kawai!
Ko kuma suna son sulhun samun mafaka ne, a ƙyale su sakata su wala a wani yanki, amma suna iya shiga wani yankin su yo ɓarna su dawo wani wurin da zai zamar masu mafaka ko tudun-mun-tsira.
Duk wata damar sulhu da gata ba wadda Masari bai yi wa Fulanin daji ba lokacin yana Gwamna ba, amma da baƙin cikinsu ya bar mulki, kuma yanzu shi Farfesa ne a kan ilmin sulhu da mummunan sakamakonsa.
Ko a farka ko wata rana sai sun jaraba tayar da wani babban garin hedikwatar ƙaramar hukuma.
Bayanan sirri sun tabbatar a baya sun sha jaraba hakan, amma sai su yi tunanin za su rasa mutane sai su yi zargin za a samu turjiya sai su fasa.
Me kake tsammanin in suka tabbatar za a yi ta gudu ne fa? Shigowa za su yi su ɗebi na ɗiba, su koma daji ko inda suke da sulhu.
Gaskiya ne sulhu kuma ya yi nasara, kamar yadda aka yi da MEND da NDVF a Niger-Delta, waɗanda manyan kwamandojin MEND suka zama yanzu su aka ba aikin kula da tsaron bututun mai.
Kamar su Oweizidei Thomas Ekpemupolo da aka fi sani da Tompolo da Mijahid Asari Dokubo.
Na je Neja-Delta ana cikin yaƙin, na kuma je ana sulhun, na je bayan samun zaman lafiya. Matsalar tana da bambanci, rubutunta na musamman ne.
Mu a nan sai mun farka mun amince da kare kai da fito-na-fito da shahada, mutanen can sun san lamarin babu daɗi, kuma ba lasa. Sannan in sun ce a zauna aka zauna zai iya amfani.
Amma zama da rayuwa suna zakuna, wasu na tumaki, zaman ƙasƙanci da izgilanci da walaƙanci ne.
Ya rage mu zabi mai yiwuwa.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
All in All social media handles..07043777779.08057777762