Katsina Times
Matashin dan siyasa, Salmanu Ahmad Gafai, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar SDP, yana mai bayyana cewa ya yanke wannan hukunci ne sakamakon damuwa da halin da talakawa ke ciki.
A cikin sanarwar da ya fitar, Gafai ya ce ya dade yana nazarin yadda shugabanni ke tafiyar da al’amuran kasa, inda ya fahimci cewa ba sa sanya muradun talaka a gaba. Saboda haka, ya ce ya yanke shawarar shiga jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) domin ci gaba da fafutukar kare hakkin talakawa.
Ya kuma jaddada cewa jam’iyyar SDP, wadda marigayi Malam Aminu Kano ya kafa da muradin kare talakawa, ta sake samun gagarumin karbuwa a yanzu, musamman bayan Sanata Babba Kaita da wasu jiga-jigan siyasa sun rungume ta.
Gafai ya bukaci matasa da sauran ‘yan kasa masu kishin talakawa da su yi duba na tsanaki kan wannan tafiya, tare da yin tunani mai zurfi kan makomarsu a siyasa.
"Dukkan mu talakawa ne, ya zama dole mu tsaya tsayin daka don kare muradunmu," in ji shi.