Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana jin daɗinsa da aikin da ke gudana na filin jirgin sama na Zamfara.
A ranar Larabar da ta gabata ne gwamnan ya zagaya tare da duba ayyukan filin jirgin sama na Zamfara, ayyukan hanyoyi, sakatariyar jihar, da gyaran da aka yi a wasu makarantu da ke Gusau, babban birnin jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa, an fara gudanar da ziyarar ne a ranar Talata a babban asibitin Gusau, wanda ake ci gaba da gyare-gyare da kuma inganta kayan aiki.
Sanarwar ta ƙara da cewa, ziyarar wani bangare ne na tsarin Gwamna Dauda Lawal na tabbatar da ingantattun ayyuka a faɗin jihar da kuma tabbatar da kammala ayyukan a kan lokaci.
“A ranar Talata ne Gwamna Dauda Lawal ya fara ziyarar aiki domin duba ɗimbin ayyukan da gwamnatinsa ta fara aiwatarwa.
“An fara ziyarar ne da Babban Asibitin Gusau, ɗaya daga cikin manyan asibitocin da aka gyara, tare da samar mata da kayan aiki a faɗin ƙananan hukumomi 14 na jihar.”
A lokacin da yake duba aikin filin jirgin sama na Zamfara, Gwamna Lawal ya ce, gwamnatinsa ba wai kawai tana gina kowane irin filin jirgin saman ba ne, amma ana ginin ne na zamani wanda zai yi fice bisa ga dukkan alamu.
“Gwamnan ya nuna jin daɗinsa da yadda aikin ke gudana, wanda ya haɗa da titin jirgi da tasha.
“Gwamna Lawal ya kuma duba hanyar garin Rawayya da ke gudana da kuma aikin gina tsohuwar Titin Kasuwa zuwa mahaɗar Chemist na Nasiha.
“Sauran ayyukan da Gwamna Dauda Lawal ya duba a halin yanzu sun haɗa da gyaran kashi na biyu na Sakatariyar JB Yakubu ta Jihar, Kwalejin Kimiyya ta Zamfara (ZACAS), da kuma Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati.”