ALMIZAN A SHEKARU 35: ABIN DA ZAN IYA TUNAWA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes04032025_222445_IMG-20250304-WA0032.jpg



Daga Danjuma Katsina

Sha’awar karance-karance ya saka ni aikin jarida. A firamare ina cikin wadanda ake sawa su karanta littafin Hausa a gaban aji. A makarantar sakandare har suna aka lakaba mani da sunan “World master story reader.”

Na shiga jami’ar Ahmadu Bello Zariya domin karatun aikin jarida a 1990. Mune ajin farko na wannan kwas din. A nan na hadu da Malam Ibrahim Musa babban Edita, kuma daya daga cikin wadanda suka kafa jaridar ALMIZAN.

Wata rana ya same ni, shi da marigayi Malam Umar Chiroma, ya fada mani cewa za su kafa jarida mai suna ALMIZAN, in bayar da nawa shawarwarin a matsayina na dalibin aikin jarida. Na bayar da nawa shawarwarin, har da maganar suna. Na ce wasu a Kano sun kaddamar da wani kamfani mai suna ALMIZANI. Daga baya sun dauki sunan ALMIZAN bayan tuntuba da suka yi, har da tattaunawa da Malam Ibraheem Zakzaky (H), wanda suka kara masu da hujjar cewa akwai bambanci tsakanin ALMIZANI da kuma MIZANI. Ya ce, wancan kamfani ne, wannan kuma jarida ce.

A jami’ar ABU Zariya na rike matsayin mai hulda da jama a na kungiyar dalibai ta MSS na jami’ar, har na zama Editan mujallar MSS ta lokacin, mukamin da na rike har na bar jami’ar. A lokaci guda Malam Ibrahim Musa suna ta aikinsu na buga ALMIZAN.

A 1991 aka yi zanga-zangar mujallar Fun Times a duk fadin kasar nan, wadda muka fara ta daga jami’ar ABU Zariya. Gwamnan Katsina na lokacin ya yi barazanar kashe Malam Yakubu Yahaya Katsina. Wannan ya sanya aka sake wata zanga-zangar. Wannan ya janyo aka kama ’yan uwa da yawan gaske, ciki har da ni.

Ina tsare a ofishin ’yan sanda na Sabon gari da ke Katsina na rubuta wata takarda a kan halin da muke ciki a inda ’yan uwa suke tsare. Wannan shi ne farkon rubutu na da jaridar ALMIZAN, wanda ya tayar da kura sosai.

Kyakkykawar danganta tsakani na da Alhaji Hamid Danlami da Malam Ibrahim Musa ya sanya suka yi shawarar saka ni cikin aikin tsundum a 1992, kuma aka ba ni aikin rubuta labarai, samowa, fassarawa da kuma duk wani aikin da aka dora mani. Aikina a lokacin zan rika bin duk jaridu, mujallu, da akan sanya ni in tsamo labaran da suka dace da tsarin jaridar. Zan saurari rediyo in zakulo labarai. In ana taro a Zariya zan rika hira da ’yan uwan da suka fito daga wurare ina rubuta labarai.

Ni na fara kirkiro tsarin fassara mai ’yanci. Zan karanta sharhi ko labarai da Turanci, sai in fahimci sakon labarin, sai in yi rubutu a kan haka. Daga baya na yi rubutu a kan wannan; na kare matakin da na dauka na amfani da fassara mai ’yanci. Yanzu hatta jami’o’i da sauran kafafen watsa labarai sun amince da fassara mai ’yanci.

A 1993 aka kirkiro da mujallar GWAGWARMAYA, kuma aka ba ni matsayin Editan ta. Ina tsara labaran mujallar, ina kuma sharhi, nazari da labarai a jaridar ALMIZAN. An kuma kirkiro da mujallar mata ta MUJAHIDAH, wadda Shaikh Abdulhamid Bello ya yi wa Edita. Ita ma na rika rubutu a cikin ta.

A mujallar GWAGWARMAYA ne na yi rubutun “Zuwa ga marubutan soyayya,” wanda marubuta suka yi wa jaridar ALMIZAN caa da mujallar da martani kala-kala, wanda lokacin kullum akwatin gidan waya din mu a cike yake da wasiku.

MANYAN HIRARKIN ALMIZAN

Farkon ALMIZAN, duk hirarrakin ta da Malaman Harkar Musulunci ne, sai kuma wadanda aka zalunta, sai wadanda ke goyon baya ko masu tausaya ma Harkar Musulunci, babu da ’yan siyasa ko masu mulki. A 1994 a wani zama da aka yi aka yanke shawarar a fada ma duk wakilan jaridar, kowa ya yi hira da wani babban Malami a yankinsu. Wadannan hirarraki na lokacin sun fadada jaridar zuwa zawiyoyi da makarantu da kungiya-kungiya.

Ni na yi hira da Malam Lawal Abubakar, wanda ya gaji Shaikh Mahmud Gumi bayan rasuwar sa. Na yi hira da Shaikh Dahiru Usman Bauchi a lokacin. Na gana da Shaikh Umar Sanda, masanin ilmin falaki da taurari. Na yi hira da Shaikh Ahmad Gumbi. Na je Kano na hadu da Mal. Muhammad Bakari muka yi hira da Shaikh Nasiru Kabara, har ya ba ni kyautar littafai. Na je Sakkwato na yi hira Waziri Junaidu.

Haka kuma Wakilan garuruwa sun yi ta turo hirarraki, wanda aka yi ta bugawa. Hirar duk ta doru ne a kan tarihin Malaman da gwagwarmayarsu ta neman ilmi. Mun rika kauce ma duk wata magana da za ta kawo rarraba kan musulmi da kuma cece-kuce. Na yi hira da marigayi Lawal Bala Kalarawi.

Hirarraki uku zan iya tunawa, daya mai tayar da hankali, daya mai armashi, daya mai ban mamaki. Mai tayar da hankalin ita ce, ni na yi magana ta karshe da Malam Turi kafin a kama shi a waki’ar Abacha ta 1996. Na same shi a gidansa na Kwarbai ya yi mana magana ta karfafa gwiwa da kuma dakewa da hadin kai a komai zai faru a gaba. Kwana daya aka ce mani an kama shi.

Ta biyu mai armashi, ita ce wadda muka yi hira da Malam Zakzaky (H), ni da Shahid Ibrahim Usman, mu uku, watanni bayan fitowar su daga gidan yari daga kamawar Abacha. Hira ta uku mai ban mamaki, ita ce hirar da na yi da Guru Maharaji na Ibadan.

Jaridar ALMIZAN ta yi manyan hirarraki. Daga cikin su akwai da tsohon Shugaban kasa Ibrahim Babangida, da tsohon Shugaban kasa Muhammadu Buhari da tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Musa ’Yar’aduwa. Haka kuma ta yi hira da tsaffin manyan ’yan siyasa irin su Malam Tanko Yakasai da Lawal Dambazau da tsaffin gwamnoni da tsaffin Sarakuna. Misali Sarkin Zazzau, marigayi Alhaji Shehu Idris da Sarkin Katsina marigayi Kabir Usman Nagogo. Manyan dattawa masu kishin kasa, wadanda suka sadaukar irin su M.D. Yusufu da manyan sojoji irin su Tukur Buratai, duk an yi hira da su a ALMIZAN.

MANYAN LABARAI

Jaridar ta buga manyan labarai da suka yi tasiri sosai a kasar nan, ba ma wani yanki na kasar nan ba. Wadanda suka shafe ni kai tsaye daga cikin su akwai: ZOBE MAI AMAN KUDI NA WANENE?

Wani labari ne da na rubuta a kan wani zobe mai aman kudi da aka tsinta a wani masallaci a jihar Katsina. Labari ne da aka kawo mani shi ta amintacciyar hanya. Na kara da nawa binciken,a na saki labarin. Ya girgiza kasar nan, an yi ta juya labarin zuwa kafa-kafa, ana canza masa salo.

Babban bakin cikina a labarin shi ne yadda aka rika daukar wani matashi wanda a lokacin yana tashen kudi, gwamnatin soja ta lokacin tana yi da shi, amma aka rika tambayar ya aka yi ya samu kudi? A labarin na ba da misalai da zai tabbtar da ba shi bane, amma makiyansa suka yi ta yada cewa shi ne.

A lokacin an yi, an yi da ni in fadi wane ne? Na ki fada. Mutum biyar kadai na fada mawa sunansa. Daga cikin su akwai marigayi MD Yusufu, wanda ya tabbatar mana da bincike ya tabbatar ba sharri nake yi ba. Mutumin da labarin ya shafa, na taba gabatar masa da kaina a wani taro a Kaduna. Sai ya kalle ni ya ce, duk bawan da ya rufa wa bawan Allah asiri, Allah zai rufa masa nasa. Nan na ji kwalla ta cika mani idanu. Mutumin, yanzu ya dade da rasuwa, kuma ya rasu da kyakkyawar shaida, duk Katsina cewa ake mutumin kirki ne.

Labari na biyu na hoton Annabi Musa (AS) da wata mujalla ta zana aka buga. Na samu mujallar ta hanyar Abdullahi Lowcost. Na rubuta labarin, na aika tare da mujallar satin da aka buga shi. Kasar nan ta dauka jaridar ALMIZAN ta buga hoton Annabin Allah.

Labari na uku shi ne na yadda ’yan JTI suka saro kan kafirin nan Gidion Akaluka a birnin Kano. Na isa Kano da yamma, na kwana. Da safe na fara binciken ya aka yi? Na gana har da Shugaban JTI na Kano a lokacin, Ahmad Shu'aibu. Na samu tabbacin me ya faru, ya aka yi lamarin?

Na dawo Zariya, na ba da labari, na kuma rubuta me na gano; na bayar aka buga. Fitar jaridar ta girgiza har da ’yan JTI da suka dauka in an tashi labarin, ba za a yi masu adalci ba. Sai ga shi labarinmu ya fi wanda suka rubuta a jaridar su adalci.

Labari na hudu na rikicin gwamnan Kano, Abdullahi Wase da gidan Kadiriyya. Gwamnatin Kano ta yi yunkurin hana taron maukibi, Shaikh Nasiru Kabara ya ce, ba su isa ba. Aka tura ni dauko rahoton. Na yi hira da Malam Nasiru Kabara a tsaye a bakin masallacin gidansa, inda ya shelanta cewa ba za su sake yarda ba a hana su taron da Allah ya halasta masu. Jaridar ta fito da hoton Malam Nasiru Kabara bisa doki da takobi a hannunsa da taken ba za mu sake yarda ba.

Labari na biyar na kisan kiyashin ’yan Tatsine a Funtuwa. A gabana aka rika kona su da rai. Mun dauki hotuna a lokacin masu tayar da hankali. Duk kasar nan, da hutunan da jaridar ALMIZAN ta buga aka rika amfani da shi. Rikici ne da ya fara daga gardama a kasuwa, ya koma kasha-kashe na duk wadanda aka ce wai ’yan Tatsine ne. Wannan gani-da-idon ya yi mani tasiri ga duk rubutuna da ayyukana na cewa, kar mu yi katanga ko shamaki da mutane. Wannan shi ne mataki mafi hatsari. Na yi wani sharhi a kan haka mai taken rikicin al’ummar gari da ’yan Tatsine, sai kuma wa? A lokacin na ga ana danna yaro cikin wuta, yana ci, yana kokarin fita, ya tsira, ana mayar da shi. Na ga rijiyar da aka cike da mutane a ciki, don kar su fito.

Labarin zargin kwartanci da aka yi ma wani dan uwa a Sakkwato ya saka ni tsaka mai wuya, kuma daga karshe ya ba ni ruwa. Wani labarin da wata mata ta yi ma Malam Yakubu Yahya takakkiya shi ne mai taken “Saboda matan banza, ’ya’ya sun casa ubansu.” Labari ne da yarinyar da abin ya shafa, ta same ni har gida ta fada mani.

Mun yi labarai manya a rikice-rikice daban-daban lokacin shari’ar su Zamani Lekwot. Na yi shigar mata na shiga kotun. Na taba shigar mata na shiga barikin soja na Zariya. Na yi shigar kiristoci na sha shiga coci.

Don samun karashen labarin da Malam Danjuma Katsina ya bayar a littafin, to maza ka mallaki naka kwafen ta hanyar shiga wannan shafin na intanet: https://selar.com/12j84m

Ko kuma ka turo kudin littafin N1000 kacal ta Opay ko Moniepoint 8037023343. Ibrahim Musa. Nan take za a turo ma littafin ta lambar da kake yin WhatsApp.

Follow Us