Muhammad Ali Hafizy, Katsina Times.
Kungiyar daliban kiwon lafiya masu zaman kansu mai suna (Coalition Of Private Health Institutions Of Katsina State Student Union Leaders), wadanda aka dakatar, sun roki gwamnati akan ta bude masu makarantun sakamakon tsawon lokacin da suka dauka na datsewar karatun su.
A yayin kai koken nasu, a ranar Laraba 26 ga watan Fabrairu 2025, a ma'aikatar ma'aikatu na jihar Katsina, wanda shugaban tafiyar tasu Lukman Abubakar ya jagoranta, a wajen shugaban ma'aikata na karamar hukumar Katsina, Alhaji Falalu Bawale, wanda ya samu wakilcin Alhaji Lawal Suleman Abdullahi, P.S Head Of Service.
Jagoran tafiyar tasu, Lukman Abubakar wanda ya samu rakiyar bangarori daga makarantun da aka dakatar din, a jawabin makasudin zuwan nasu, ya bayyana matukar godiyar shi ga gwamnatin jihar Katsina game da matakin da ta dauka da tsaftace harkar lafiya a jihar, sannan ya yaba ga kwamitin da suka gudanar da bincike a zagaye na farko da na biyu.
Lukman Abubakar ya roki gwamnati akan ta waiwayi Makarantun wadanda suka sake cika ka'idojin da kwamitin suka sanya masu, ya bayyana cewa kwamitin ya sake komawa a karo na uku yayi bincike ga Makarantun amma har yanzu tsawon watanni biyu basu ji wani sakamako game da binciken ba, dalilin haka ne suke rokon gwamnatin akan ta sanya baki cikin lamarin domin ganin sun dawo sun cigaba da karatu.
A jawabin da ya mayar masu Alhaji Lawal Suleman Abdullahi P.S ya nuna matukar jin daÉ—in shi game da yunkurin da daliban suka yi na tuntuba game da mataki da ake kai, ya shaida masu cewa gwamnati ta damu da halin da suke ciki amma komi ana yin shi ne domin ganin a tsaftace masu karatun nasu.
Ya bayyana masu cewa sun karbi koken nasu, sannan kuma zasu cigaba da bibiyar halin da ake cikin har zuwa lokacin da za'a bude masu makarantun.