Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
Malam Abubakar Karawa, mazaunin karamar hukumar Dutsinma ta jihar Katsina, yana cikin mawuyacin hali bayan da wani jami'in sa kai na Civilian Joint Task Force (CJTF) ya harbe shi, wanda hakan kuma ya yi sanadin mutuwar wani dalibi na Jami’ar Tarayya ta Dutsinma (FUDMA).
Da yake zantawa da Katsina Times a ranar Talata, Malam Abubakar ya bayyana cewa tun ranar Lahadi, 23 ga watan Fabrairu, kimanin awanni hamsin kenan, harsashi yana nan a jikinsa ba tare da samun taimakon gaggawa ba. Ya ce har yanzu bai samu kulawar da ta dace daga hukumomin lafiya ko na tsaro ba, lamarin da ke barazana ga rayuwarsa.
Abubakar ya ce lamarin ya faru ne lokacin da yake dauke da wani dalibi daga jami’ar FUDMA da nufin kai shi unguwar Kashe Naira da ke cikin garin Dutsinma.
"Da muka iso, sai dalibin ya ce in jira shi ya fito, don mu koma tare. Bayan ya fito muka hau mashina sai muka ci karo da jami’an Yan banga (CJTF) da motarsu. Mun wuce ba tare da sun tsaida mu ba, don haka na raba su na wuce. Amma kafin mu ankara, sai kawai na ji mun kife kasa," in ji shi.
Ya ci gaba da cewa:
"Na ji dalibin yana ihu yana cewa: ‘Wayyo Allah, sun kashe ni! Wayyo Allah, sun kashe ni!!’ Ni kuma ban farga da komai ba sai da na ji kafata ta sage, na kasa motsawa. Ashe harbi ya same ni."
Abubakar ya ce ba su aikata wani laifi da zai sa a harbe su ba, domin ba su yi yunkurin tserewa ko nuna wani barazana ga jami’an tsaron ba.
"Wajen da abin ya faru unguwa ce cike da mutane, ba wani shinge ba ne na jami’an tsaro. Saboda haka babu wata hujjar da za ta sa in tsaya a wurin jami’an tsaro a cikin irin wannan yanayi."
Abubakar ya yi kira ga hukumomi, musamman gwamnatin jihar Katsina, da su taimaka masa domin yana cikin mawuyacin hali.
"Tun da aka kawo ni asibiti, babu wanda ya zo ya duba lafiyata ko ya tausaya min, sai mutum daya kacal—dan majalisarmu na Dutsinma, wanda ya bada naira dubu hamsin. Amma har yanzu ba mu da abinci, balle mu samu magani."
Idan za a iya tunawa, a ranar Lahadi, 23 ga watan Fabrairu, jami’an CJTF sun harbi wani dalibi mai shekarar karshe a jami’ar FUDMA, wanda hakan ya yi sanadin mutuwarsa. Wannan lamari ya haddasa zanga-zanga daga dalibai tare da kone-kone a kan titunan garin Dutsinma.
Har yanzu dai ba a samu cikakken bayani daga hukumomin tsaro kan dalilin harbin Abubakar Karawa da dalibin jami’ar FUDMA ba, amma sun tabbatar da suna gudanar da bincike.