‘Yan Sanda Sun Fara Bincike Kan Harbin da Ya Yi Sanadin Mutuwar Dalibi a Dutsinma

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes24022025_132648_Nigeria-Police-Force.jpeg


Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta fara bincike kan harbin bindiga da ya yi sanadin mutuwar wani dalibi mai matakin karatu na 400 a Jami’ar Tarayya ta Dutsinma, tare da jikkata wani mai babur.

Bayanan farko sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar 23 ga Fabrairu, 2025, da misalin karfe 11:26 na safe, lokacin da wani dan kungiyar sa-kai ta CJTF, da ke cikin wata motar Hilux, ya harba bindiga kan wani fasinja mai suna Sa’idu Abdulkadir da kuma mai babur da yake dauke da shi.

Jami’an tsaro sun hanzarta kai wadanda abin ya shafa zuwa Asibitin Gwamnati na Dutsinma, inda daga bisani aka garzaya da Sa’idu zuwa Asibitin Kashi na Katsina, amma likitoci suka tabbatar da mutuwarsa bayan isarsa.

Rundunar ‘yan sanda ta bayyana damuwarta kan lamarin tare da tabbatar da cewa za a yi adalci. Hakanan, suna aiki tare da mahukuntan jami’a da sauran masu ruwa da tsaki don gano wadanda suka aikata harin tare da daukar matakin da ya dace.

DSP Abubakar Sadiq Aliyu, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda ta Jihar Katsina, ya ce za a ci gaba da sanar da al’umma cigaban binciken da ake yi.

Follow Us