Cikakken sunansa Alhaji Abbas, mutumin Galadunchi da ke cikin garin Katsina. Ya kasance shahararren ɗan kasuwa, manomi, kuma makiyayi.
A wata hira da na yi da Muhammadu Nata’ala, ɗan Alhaji Mamuda (Mudi), wanda shi ne ɗan Marigayi Alhaji Labo Legas Kangiwa, ya bayyana cewa marigayin na daga cikin manyan ‘yan kasuwa na farko a Katsina. Kasuwancinsa ya shafi sayar da turaruka da kayan masarufi, ciki har da Mai Aku, Alkalin Goma, Dan Goma, Kafin-Kafi, Wardi, Kafi Sallama, Zawwati, da sauran kayayyaki.
A zamaninsa, sarakuna da hakimai sun fi sayayya a shagon nasa, musamman lokacin bukukuwan Sallah. Ya taka rawar gani wajen habbaka kasuwanci a bakin kasuwa, wanda hakan ya taimaka wa sanin sunan kasuwar har zuwa yau.
Lokacin da kasuwar Arewa Textile da ke Kaduna ta fuskanci ƙarancin kaya, Alhaji Labo Legas kan tafi har Lagos don samo hajojinsa. A wasu lokuta, yana shafe watanni uku a can kafin ya samu kaya ya dawo gida.
Daga cikin manyan abokan kasuwancinsa akwai:
Alhaji Labo Legas ya tafi aikin Hajji a lokacin da jirgin Makka bai fara zuwa Kano ba. Ya yi tafiyar tare da Alhaji Abarshe (Mahaifin Barau Yaro) da Alhaji Halilu Kangiwa, inda ya dawo gida ne a shekarar 1956, bayan da jirgin Makka ya fara sauka a Kano.
Ya kasance babban manomi mai gonaki biyar a tsakanin:
A kasuwanci, yana da shaguna biyar a tsakanin Kangiwa da bakin kasuwa. Haka nan, yana da gidaje kimanin 90 daga bakin kasuwa zuwa Galadunchi, har ma akwai unguwa a Galadunchi da aka sanya wa sunansa.
Alhaji Labo Legas ya kasance mai kyauta da jin ƙai. Yana bai wa ma’aikatansa gidaje kyauta, musamman waɗanda ke taimaka masa a gine-gine da aikin gona. Rabin makabartar Dan Taku Tsohuwa ta kasance gonarsa ce, wacce ya ba da sadaka domin Sadakatul Jariya.
Baya ga haka, ya gina masallatai da rijiyoyi don neman lada daga Allah.
Alhaji Labo Legas ya rasu yana da matan aure uku da ‘yan uwa gida uku. Ya bar babban tarihi a fannin kasuwanci, noma, da hidima ga al’umma, wanda har yanzu ake tunawa da shi a Katsina.
Labbo Kundum
Fans
Fans
Fans
Fans