Tarihin Kayan Sawa na Gargajiyar Hausawa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes12022025_092814_FB_IMG_1739352227374.jpg


A baya, kafin zuwan addinin Musulunci, Hausawa ba su da wata takamaiman sutura face warki da ganye domin rufe jikinsu. Sai dai da shigowar Musulunci da tasirin al'adu daga Larabawa da wasu kabilu daga Masar, Hausawa sun fara amfani da sutura masu rufe al'aura da kuma kayayyakin ado. Daga cikin wadannan riguna akwai ’yar Tambutu, Jabba, Kaftani, Kubta, da wanduna iri-iri. Haka kuma, an samar wa mata zanne (gyauto), mayafi (gyale), dankwali, da riguna don su dace da sabon tsarin rayuwa.

Hausawa kuwa, bayan sun karɓi waɗannan sutura daga Larabawa da Nufawa, sun ƙirƙiro nasu nau'in tufafi da suka dace da yanayin zamantakewarsu. Daga cikin irin waɗannan sutura akwai ’yar shara, taguwa, aganiya, fatari, da bante. An ce Hausawa sun aro bante daga Nufawa, wanda ya zama riga mai muhimmanci a rayuwarsu ta yau da kullum.

Ire-Iren Kayan Sawa na Hausawa

  1. Babban Riga

    • Gwari
    • Sace
    • Shakwara
    • Aganiya
  2. Rigunan Maza da Mata

    • ’Yar Tambutu
    • Doguwar Riga
    • Fanjama
    • Hartin
    • Jallabiyya
    • Zuleka
    • Kaftani
    • ’Yar Ciki
    • Dahariya
    • ’Yar Shara
    • Zuhuni
    • Falmaran
  3. Wanduna

    • Tsala
    • Fanyama
    • Bulus
    • Dan Itori
    • Dantunis mai Kamun Kafa
    • Kwarjalle
  4. Huluna

    • Dankwara
    • Bakwala
    • Damanga
    • Habar Kada
    • Facima
    • Zanna
    • Kube
    • Zita
  5. Rawani

    • Harasa
    • Bakin Fara
    • Dankura
    • Mubarrashi
  6. Takalma

    • Dangarafai
    • Sambatsai
    • Fade
    • Mai Gashin Jimina
    • Dan Maroko
    • Huffi
  7. Zanen Mata

    • Saki
    • Bunu
    • Bakurde
    • Gam Sarki
    • Tsamiya
    • Dantofi
    • Fatari
    • Saroda
    • Mukuru

Sana’o’in Gargajiya na Hausawa

Hausawa suna da sana’o’i da yawa da suka samo asali tun zamanin da, kuma har yanzu wasu daga cikinsu na ci gaba da kasancewa. Daga cikin su akwai:

  • Kasuwanci da Fatauci
  • Saka da Rini
  • Farauta da Jima
  • Noma da Kiwo
  • Kira da Sassaka
  • Dukanci da Gini
  • Fawa da Wanzanci

Muhalli da Tsarin Gine-Ginen Hausawa

Gidajen Hausawa sun kasu kashi-kashi bisa ga bukatun rayuwa da kuma yanayin zamantakewa. Daga cikin ire-iren gine-ginensu akwai:

  • Bukka
  • Tsangaya
  • Dakin Hayi
  • Shigifa ko Soro
  • Kudandan ko Rudu
  • Kago

Kammalawa

Sutura na daga cikin manyan alamomin al’adar kowace al’umma. Hausawa sun sami sauye-sauye a tsarin kayansu na sawa sakamakon shigowar Musulunci da hulɗarsu da sauran al’ummomi. Duk da haka, sun ci gaba da riƙe al'adunsu tare da ƙirƙiro sutura da kayayyakin da suka dace da yanayinsu. Har ila yau, sana’o’i da tsarin gine-ginen Hausawa na daga cikin al’adun da suka nuna girmansu da hikimarsu tun zamanin da har zuwa yau.

Follow Us