Sheikh Iyal Gafai Ya Zama Babban Limamin Masallacin Juma’a na Mangal Katsina

top-news

Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times 

An nada Sheikh Iyal Gafai a matsayin Babban Limamin Masallacin Juma'a na Mangal dake Unguwar Tayoyi, cikin birnin Katsina, wanda ke cikin tarihi a matsayin sabon shugaba mai cikakken kwarewa wajen jagorantar al'umma. Wannan nadin ya kasance ne a ranar Asabar, 1 ga Watan Fabrairu, 2025, wanda ya yi daidai da 3 ga watan Sha'aban, 1446.

Mai martaba Sarkin Katsina, Alhaji Dr. Abdulmumini Kabir Usman, CFR, ya yi farin cikin tabbatarwa da Sheikh Iyal Gafai wannan mukami mai daraja a fadar sarkin, da ke kofar Soro, cikin birnin Katsina. A wannan taron, mai martaba sarkin Katsina ya nada Sheikh Iyal Gafai a matsayin Babban Limamin Masallacin Juma'a na Mangal, tare da nada wasu manyan mutane 19 a matsayin masu rike da sarautun gargajiya a cikin al'umma. 

A cikin jawabinsa, mai martaba Sarkin Katsina ya ja hankalin sabbin shugabanni game da nauyin da Allah ya dora musu, yana mai karfafa musu gwiwa da cewa, su gudanar da aikinsu na shugabanci da gaskiya da adalci, domin tabbatar da ci gaban al'umma da kyautata zamantakewa.

Sheikh Iyal Gafai, wanda a baya ya kasance Na'ibin Limamin Masallacin Juma'a na Mangal kafin rasuwar tsohon Limamin, Sheikh Abbati Katsina, yanzu ya karbi wannan nauyi mai girma, inda ake sa ran zai ci gaba da jagorantar masallacin a matsayin babban limamin.

Follow Us