Ita Dai Gaskiya Kodayaushe Sunanta Gaskiya.. -Shugaban Jam'iyyar PDP Katsina

top-news

Jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina ta ƙarba tare da amincewa da karfafawa da gwamna jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa  ya yi na cewa jihar Katsina ta PDP ce kuma zata cigaba da kasancewa ta PDP.

wannan kalamai suna kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban jam'iyyar PDP na jihar Katsina Malam Nura Ahmadi Kurfi ya fitar inda ya ce hakika wannan batu ne na karfafawa ga dukkanin wani ɗan jam'iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina baƙi ɗaya.

A cewar sa, Idan za a iya tunawa, tun daga shekarar 1999 jihar Katsina dai 'ya 'yan jam'iyyar PDP ne suka mulke ta da suka haɗa da Marigayi Umar Musa Yar'adua da Ibrahim Shema da kuma Aminu Bello Masari sai kuma na yanzu Dikko Raɗɗa, cikin su wanene ba ɗan PDP ba?

Hon. Nura Ahmadi ya ƙara da cewa idan za a yi tunawa a zaɓen 2023 jam'iyyar adawa ta PDP ce ta lashe zaɓen shugaban ƙasa a jihar Katsina, sannan duk mun san abinda ya faru a zaɓen gwamnan da ya gabata.

Hon. Nura Ahmadi Kurfi wanda ya bayyana cewa lokacin da gwamnan Katsina ya ayyana cewa jihar Katsina ta PDP ce, kawai yana bayyana gaskiyar al'amarin da ke cikin zuciyarsa ta hanyar yin magana da mutanen Katsina da Daura

Ya ƙara da cewa, kamar yadda gwamna Malam Dikko Raɗɗa ya san gaskiya, kuma ya san inda ya kamata ya faɗe ta, to ya bayyana ta a gaban shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Abdullahi Umar Ganduje da sauran al'ummomi.

"Muna fatan cewa wannan subul da baka da Dikko Raɗɗa ya yi ya zama ɗan ba na kawo ƙarshen mulkin APC a jihar Katsina. Sannan ya kamata gwamnati ta fara abinda ya kamata ta hanyar samar da kyakkyawar shugabanci ta yadda al'ummar Katsina za su kasance cikin tsaro sannan su more romar dimokuraɗiyyar kamar yadda suka amfana a lokacin mulkin PDP" inji shi