Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Kurfi da Dutsinma Ya Kai Ziyara Ta Musamman a Kurfi, Ya Gabatar da Muhimman Ayyuka Masu Amfani Ga Al'umma
- Katsina City News
- 25 Jan, 2025
- 73
A ranar Juma'a, 24 ga watan Janairu 2025, Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Kurfi da Dutsinma, Hon. Aminu Balele Dan Arewa, ya kai ziyara ta musamman a Karamar Hukumar Kurfi, inda ya gudanar da muhimman ayyuka da suka shafi cigaban al'umma, musamman a bangaren ilimi da addini.
A yayin wannan ziyara, Hon. Aminu Balele Dan Arewa ya gabatar da wani gagarumin shiri na tallafa wa harkar ilimin addini a fadin kananan hukumomin Kurfi da Dutsinma. A karkashin wannan shiri, ya biya kudin makarantar Islamiyya na tsawon shekara guda ga dukkan Islamiyyun da ke cikin yankin. Wannan tallafi ya shafi kimanin matan aure 2,750 daga Islamiyyu 56 da ke fadin mazabar, inda 34 daga cikin wadannan Islamiyyu suke a Karamar Hukumar Kurfi.
Bugu da kari, Hon. Aminu Balele Dan Arewa ya sanar da karin alawus-alawus ga Limamai da Ladanai a kananan hukumomin Kurfi da Dutsinma, a wani yunkuri na inganta rayuwar ma'aikatan addinin Musulunci da bada gudummawa wajen kara bunkasa harkokin addini a yankin.
A yayin ziyarar tasa, Dan Majalisar ya kuma kai ziyarar ta'aziyya ga al'ummar Kurfi saboda rashin wasu daga cikin manyan 'yan yankin da suka rasu. Hakazalika, ya kai ta'aziyya ga Hon. Zaharaddini Usman, Dan Majalisar Jiha mai wakiltar Kurfi, bisa rasuwar mahaifinsa.
Hon. Aminu Balele Dan Arewa ya jaddada kudirinsa na ci gaba da wakiltar al'umma bisa gaskiya da rikon amana, tare da kara azama wajen gudanar da ayyukan cigaba masu ma'ana ga yankin Kurfi da Dutsinma. Wannan ziyara ta nuna yadda yake mai da hankali wajen tallafa wa al'umma, musamman a fannin ilimi da addini, wadanda ke da matukar muhimmanci ga cigaban zamantakewar jama'a.