Dogo Gide ya kashe mayaƙan Boko Haram guda 20, ya kwace makamai
- Katsina City News
- 24 Jan, 2025
- 96
Shahararren shugaban 'yan fashi, Dogo Gide, ya kashe mayaƙan Boko Haram guda 20 a wani ƙauye dake tsakanin jihohin Neja da Zamfara, kamar yadda jaridar Daily Trust ta gano.
Mayaƙan Boko Haram ɗin, waɗanda ake zaton suna aiki ƙarƙashin wani babban shugabansu mai suna Sadiku, sun yi ƙoƙarin kai hari kan Dogo Gide. Sai dai Gide da mayaƙansa sun shiga fafatawa da su, inda suka kashe guda 20 daga cikin su tare da kwace manyan makamai.
Fafatawar ta faru ne a dajin Kwatankoro, wanda ke kan iyakar jihohin Neja da Zamfara.
A wani bidiyo da ya bayyana kwanan nan, an ga Dogo Gide yana jawabi inda ya nuna makaman da aka kwace, waɗanda suka haɗa da bindigogi AK-47 guda goma, RPG, wayoyin hannu, da katin shaida da ake zaton na bangaren Sadiku ne.
"Aƙalla mayaƙansu guda 20 sun mutu, yayin da namu ɗaya ne kawai ya ji rauni," inji Gide, yana zargin mayaƙan Sadiku da yin amfani da sunan jihadi wajen cin zalin fararen hula.
Rikicin da ke tsakanin Dogo Gide da mayaƙan Boko Haram ya nuna yadda ake samun sabani a cikin ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi a yankin, inda rashin jituwa da neman iko ke haifar da tashe-tashen hankula.
Rahotanni sun bayyana cewa kiyayyar Gide ta samo asali ne daga kisan ɗan uwansa mai suna Sani a shekarar 2023, wanda ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka yi, lamarin da ya sa Gide ya yanke hulɗa da ƙungiyar tare da ɗaukar fansa.
Tun daga lokacin, Gide ya mayar da hankali wajen fatattakar mayaƙan Boko Haram daga yankinsa, musamman a karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja, inda ya rusa shingayen da mayaƙan suka kafa.
Jaridar Daily Trust ta kuma bayyana cewa kwanan nan Gide ya yi kira ga mutanen da rikici ya raba da muhallansu da su koma gida, yana mai alkawarin dawo da zaman lafiya da kuma neman yafiyar al’umma.