KUNGIYAR "NATIONAL HUMAN RIGHTS" TA KAI KARAR JAMI'IN HIZBA WAJEN KWAMISHINAN 'YAN SANDA A KATSINA
- Katsina City News
- 22 Jan, 2025
- 120
Wata kungiya mai rajin kare hakkin dan Adam, National Human Rights, ta kai karar wani jami'in Hizba mai suna Muhammadu Shuaibu, gaban Kwamishinan 'Yan Sanda na jihar Katsina. Wannan karar na dauke da zargin cin zarafin wasu mutane uku: Kabir Mamman, Shamsu Lawal, da Hadiza Bala.
Zargin ya fito ne daga wata takarda mai kwanan wata 18 ga Disamba, 2024, wadda kungiyoyi suka aika wa Kwamishinan 'Yan Sanda tare da kwafi ga jaridar Katsina Times. A takardar, an bayyana cewa akwai hotuna da bidiyo da ke tabbatar da zargin cin zarafin.
Takardar ta bayyana cewa jami'an Hizba sun kama Hadiza Bala bisa zargin yawon banza. Sannan, yayin bincike, an zargi jami'an da cin zarafin Hadiza da sauran 'yan uwanta biyu da suka je neman dalilin da ya sa aka kama ta.
Kungiyar ta kara da ikirarin cewa Hadiza ta sha tsangwama har sun karya kafarta, yayin da dan uwanta ya samu mummunan rauni a bayansa sakamakon dukan da aka yi masa.
Shugaban kungiyar ya bayyana wa jaridar Katsina Times cewa suna kira ga 'yan sanda su kammala bincike tare da kai wadanda ake zargin kotu domin bin hakkin wadanda aka zalunta.