Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya Reshan Jihar Kaduna Ta Yi Watsi Da Sabuwar Dokar Gyaran Haraji
- Katsina City News
- 21 Jan, 2025
- 96
Gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya (CNG) reshen Jihar Kaduna, ta nuna rashin amincewarta da sabuwar dokar gyaran haraji tare da kiraye-kiraye ga gwamnati ga karin shawarwari kafin a zartas da kudirin dokar gyaran haraji da ke gaban Majalisar Tarayya.
A cikin wata sanarwa da suka fitar bayan taron tattaunawa, wadda Comrade Muhammed Sanusi Ali ya sa wa hannu a madadin wasu kungiyoyin al’umma da na agaji a Kaduna, an bayyana cewa: “An yi watsi da kudirin dokar gyaran haraji saboda rashin adalcin da ke cikinta da kuma illolin da zai iya haifar wa wasu yankuna da bangarorin tattalin arziki daban-daban.”
Sanarwar ta jaddada cewa dole ne gyaran harajin ya samu cikakkiyar shawara tare da dukkan yankuna da mahimman masu ruwa da tsaki, ciki har da kungiyoyin al’umma, makarantu, da kananan hukumomi, don tabbatar da tsarin da ya dace da kuma adalci.
Karin Nauyin Haraji: An bayyana cewa, tsarin sabuwar manufar kudi na kasa na iya jefa karin nauyin haraji kan ‘yan kasa, musamman masu karamin karfi. Idan ba a tsara shi yadda ya kamata ba, wannan gyaran zai kara yawaitar rashin daidaito da kuma rage damar samun ci gaban tattalin arziki.
An kuma bayyana cewa, a daidai lokacin da ‘yan Najeriya ke fama da tasirin cire tallafi da daidaita darajar Naira, wanda ya haddasa tashin gwauron zabi na farashin kayayyaki da ayyuka, wannan gyaran zai kara tsananta halin kunci.
Rashin Jin Dadi da Tashin Hankali: Sanarwar ta gargadi cewa idan aka dauki gyaran harajin a matsayin mara adalci ko mai tsanani, hakan na iya haifar da yawaitar rashin jin dadi a tsakanin jama’a da kuma rasa amincewa ga hukumomin gwamnati. Tarihi ya nuna cewa matsalolin tattalin arziki na iya haifar da tashe-tashen hankula da suka dakile ci gaba a al’umma.
Haraji a Tsakiyar Talauci: An tambaya cewa idan aka ce kamfanoni ne kawai za su biya karin haraji, ta yaya za a hana su kara farashin kayayyaki da ayyuka don daidaita kudaden VAT? Shin akwai wata hanya ta sarrafa farashin kaya? Duk wadannan abubuwa na iya kara yawaitar rashin daidaito a samun kudin shiga tsakanin al’umma.
Haka kuma, sanarwar ta yi nuni da muhimmancin hukumomi kamar TETFUND, NITDA, da NASENI, wadanda suka kasance ginshiki wajen bunkasa ilimi, fasaha, da masana’antu a Najeriya. Taron ya bukaci a dakatar da duk wani yunkuri na rage kudade ko sake fasalin wadannan hukumomi.
Bugu da kari, an bada shawarar a kara karfafa kudaden shiga da ayyukan wadannan hukumomi, don su samu damar magance manyan kalubale, ciki har da bincike, kirkire-kirkire, da gina karfin fasaha, wanda shi ne hanya mafi dacewa don ci gaba mai dorewa a kasa.