Jirgin MAX AIR Da Ya Samu Tangardar Inji Ya Ya Sauka Lafiya A Filin Saman Maiduguri
- Katsina City News
- 05 Dec, 2024
- 280
Katsina Times
Jirgin saman MaxAir mai lamba VM1623 ya dawo filin jirgin sama na Maiduguri bayan gano matsala a injin yayin tashi. Matukin jirgin ya yanke shawarar dawowa bisa tsari na kare lafiya da amincin fasinjoji, inda aka kashe injin da ya samu matsala, kuma jirgin ya sauka lafiya ba tare da wata barazana ga fasinjoji da ma’aikata ba.
A bisa jajircewar kamfanin MaxAir wajen kare lafiyar fasinjoji, an aika wani jirgi zuwa Maiduguri cikin gaggawa domin tabbatar da cewa fasinjoji sun isa inda suke nufi ba tare da jinkiri mai yawa ba. Kamfanin na bakin cikin wannan rashin jin daɗi da aka samu, kuma yana godiya ga hakurin fasinjojin.
MaxAir tana aiki tare da hukumomin sufurin jiragen sama don gano musabbabin matsalar injin. A matsayin daya daga cikin manyan kamfanonin jiragen sama a Najeriya, MaxAir na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da mafi ingancin tsaro da aiki domin samun cikakken amincewar fasinjoji.