YAKIN BURMI (1903) DA TAWAYEN SATIRU (1906).
- Katsina City News
- 04 Dec, 2024
- 398
Yakin BURMI na shekarar 1903 da Kuma Tanzoma ko Kuma Tawayen SATIRU suna daya daga cikin Manyan Gumurzun da akayi tsakanin Turawan mulkin Mallaka da mabiyan Daular Sokoto ko Kuma Daular Usmaniyya.
YAKIN BURMI( BATTLE OF BURMI 1903).
Bayan da Turawan mulkin Mallaka suka ci Sokoto da Yaki a Filin Giginya a cikin shekarar 1903, sai Sarkin Musulmi Attaru Ahmadu na I, ya bada umarni da akayi gudun Hijira zuwa Saudiyya. Yayi bayani cewa da su rayu a karkashin mulkin Turawa Kara sunyi gudun Hijira shi ya fiye masu Alheri. Mutanen da dama daga fadin Daular Usmaniyya amsa wannan umarni na Sarkin Musulmi Attahiru na I, mabiya Daular Usmaniyya daga Katsina, Kano, Zazzau da sauran sassa na Daular Sokoto sun ansa Umarnin Sarkin Musulmi.
Daga Sokoto Sarkin Musulmi Attahiru na I, suka Fara wannnan yunkuri na gudun Hijira, inda suka rika taruwa a wani Gari Mai suna Burmi Wanda ke cikin Jihar Gombe ta yanzu. Anan Burmin ne Turawan Mulkin Mallaka suka tarbesu, sukayi masu zobe, aka asake gwabza wani sabon Yakin Wanda ake cema Yakin BURMI( Battle of Burmi). A wurin wanna Yakinne Sarkin Musulmi Attahiru na I, yayi Shahada tare da wasu mabiyan shi, su wajen (200) har ya zuwa yanzu Kaburburan su suna can a Garin Burmi cikin Jihar Gombe. Bayan wadanda sukayi shahada, Turawan mulkin Mallaka sun Kama wasu da dama daga cikin su akwai Sarkin Tijjani Muhammad Albashir Wanda yazo daga Daular Tokolor( Tokolor Empire), a sanadiyyar mamayar da Turawan Faransa suka yima Daular. Anan Sokoton Yakin Burmi ya rutsa dashi, ance shi Muhammad Albashir Turawan mulkin Mallaka sun kaishi a Lokoja a matsayin dan gudun Hijira an tsare shi tareda wasu sauran Sarakunan Daular Usmaniyya da suka yima Turawa Tawaye. Ta bangaren Turawan Ingila an kashe Kwamandan Turawan a wajen Yakin Burmin Mai suna Major Mash tare da wasu sauran Turawan, shima Kabarin shi na can a garin Burmin.
Yakin Burmi shine Yaki na karshe tsakanin Turawan Mulkin Mallaka da Mabiya Daular Usmaniyya Wanda aka gwabza acikin shekarar 1903.
TAWAYEN SATIRU( SATIRU REVELION).
Acikin shekarar 1906 ne aka samu Tawaye a SATIRU dake cikin Sokoto. Wannan wani yunkuri ne Wanda ya bullo Yana Fada da mulkin Turawa da Kuma akidansu.
An samu Malaman Addinin suna waazi akan .cewa haramunne Musulmi su rayu akan mulkin Turawa. Sannan Kuma suka rika Kira akan kada a bada Haraji ko Zakka ga gwamnatin Turawan mulkin Mallaka. Wannan ya jawo babbar Tarzoma a Sokoto wadda tayi sanadiyyar Mutuwar Turawan mulkin Mallaka da dama, daga cikin su akwai Captain Hillari, mukadashin Rasdan da Mataimakin shi da wasu sauran Manyan Sojoji na Turawa duk sun rasa rayukansu. Wannan yasa dole Turawan mulkin Mallaka suka nemi dauki daga sauran Garuruwan da suke mulka kamar Katsina, Kano, Zazzau da sauransu, aka samu aka murkushe Tanzoma SATIRU.
Alh. Musa Gambo Kofar soro.