MADUGUN TAWAYE YOMI JONSON YA MUTU ......Mun san juna sosai, Dan sa aboki na ne.
- Katsina City News
- 30 Nov, 2024
- 250
Daga Ɗanjuma Katsina
Ɗan tawayen ƙasar Laberia, Yomi Jonson, ya yi suna lokacin da ya kashe shugaban ƙasar, Samuel K. Doe. Daga baya, bisa wata yarjejeniyar zaman lafiya ya baro ƙasar ya dawo Nijeriya.
A Nijeriya ya tuba, kuma har ya kafa coci a Legas ya zama babban Fasto na cocin da ya kafa.
Ya rubuta wani littafi wanda ya bayyana tarihin rayuwarsa da gwagwarmayar tawayen da ya jagoranta a ƙasar Laberia.
Ina tsammanin da yana gudun hijira a Nijeriya cikin manyan iyayen gidansa, shi ne maigidana marigayi MD Yusufu.
Ta hanyar Ogana MD Yusufu na san shi, har na kan je gidansa a Legas hira, ko in ya zo Abuja ya kira ni mu haɗu.
Daga tarayya ta da shi na san yadda 'yan tawaye ke tunani. Me ya sa sukan zama marasa imani? Ya ake kafa ƙungiyar tawaye? Ya ake samun gudunmuwar makamai da kuɗi?
Jonson ya faɗa mani gaskiyar me ya faru a kama Samuel Doe? Da gangan ya kashe shi?
Daga cikin amsar da ya ba ni ita ce, ya yi masa ba-zata ne, kuma bisa aminci ya shigo wurin da Samuel Doe yake.
A lokacin ƙasashen duniya sun yi amanna, mutuwar Doe ita ce zaman lafiya ga ƙasar Laberia, kuma ba a iya cin sa da yaƙi. Sai dai a kashe shi ta hanyar yaudara.
Na biyu ya ce shi bai kashe Doe ba. Doe ƙasƙancin da aka yi masa ya sanya ya kashe kansa a 'toilet' ta hanyar buga kansa a bango.
Jonson ya koma Laberia da zama bayan an kama Charles Taylor a Nijeriya yana ƙoƙarin gudu, bisa zargin ya saɓa wata yarjejeniyar ƙasa da ƙasa ta ba shi mafaka a Nijeriya.
Jonson ya gayyace ni zuwa ƙasar Laberia har sau uku, amma Allah bai ba ni ikon zuwa ba.
Mutum ne mai tausayi, kuma Gwarzo ne. Yana da son talakkawansa.
Har ya mutu bai taɓa faɗuwa zaɓe ba. Kuma duk shugaban ƙasar da ya goya wa baya sai ya kai labari a ƙasar.