TATSUNIYA: Ga Ta Nan, Ga Ta Nanku; Labarin Ladi Da Dodo
- Katsina City News
- 19 Nov, 2024
- 330
Akwai wata yarinya mai kyau wadda take tare da iyayenta a wani ƙauye mai suna Yana. Sunanta Ladi, kuma ta shahara da kyawun surarta da murmushinta mai cike da so da sha’awa. Ladi da iyayenta suna makwabtaka da surukan Gizo, waɗanda suka fi dacewa a ce ba sa son shiga harkokin mutane.
Wata rana, kawayen Ladi suka zo gidansu domin su tafi cin kadanya a bayan gari. Yayyenta kuwa suka ji inda za ta, sai suka gargaɗe ta kada ta tafi, domin sun san wani mummunan Dodo yana kai wa mazauna Yana hari a lokacin da suka fita bayan gari. Sai dai, Ladi ta kafe, ta nace sai ta tafi. Duk da gargaɗin iyayenta da yayyenta, ta ɗauki sanhon zuba kadanya tare da kawayenta suka nufi bayan gari.
Sun isa gindin wata babbar kadanya mai ɗauke da ’ya’ya masu ban sha’awa. Kowacce daga cikinsu ta hau bishiya tana zubar kadanya don ta debi nata rabon. Suna cikin wannan yanayi sai ga Dodo ya bayyana daga nesa ya tsuguna ƙarƙashin bishiyar, ya ce:
“Ku sauko, ku ’yan mata, in cinye ku!”
Nan take hankalinsu ya tashi, suka kama kuka saboda tsoro. Kowacce ta kasa magana saboda dimauta. Sai dai wata daga cikinsu mai wayo ta fara waka tana cewa:
“Dodo, Dodo, ba ni ce Ladi ba,
Ladi fara ce, kyakkyawa,
In ta yi dariya, nono ne ke zuba,
In ta yi murmushi, madara ce ke zuba.”
Da Dodo ya ji wannan waka, sai ya yi gunj yana cewa:
“Sauko, ’yata, ba ke nake so ba,
Da Ladi nake, zan kakkarya ta,
In sha madararta da ke zuba.”
Nan take wadda ta fara waka ta samu damar sauka daga bishiyar, ta kama hanya ta gudu gida. Sai wata daga cikinsu ta ɗauki waka tana cewa:
“Dodo, Dodo, ba ni ce Ladi ba,
Ladi fara ce, kyakkyawa,
In ta yi dariya, nono ne ke zuba,
In ta yi murmushi, madara ce ke zuba.”
Dodo ya sake cewa:
“Sauko, ’yata, ba ke nake so ba,
Da Ladi nake, zan kakkarya ta,
In sha madararta da ke zuba.”
Kamar yadda aka yi da farko, ita ma ta sauko daga bishiyar ta tsere gida. Haka aka yi har duk sauran ’yan matan suka tsere, saura Ladi ita kaɗai.
Ladi ta yi kuka saboda tsananin tsoro. Sai ga wani tsuntsu ya sauka kusa da ita, ya tambaye ta abin da ya faru. Ladi ta ba shi labarin yadda kawayenta suka gudu, kuma yanzu Dodo yana jiranta ta sauko domin ya halaka ta. Tsuntsun ya tausaya mata, ya ce zai taimake ta. Ya tambaye ta inda gidansu yake, kuma ta yi masa kwatance. Tsuntsun ya nufi gida ya shaida wa iyayenta halin da Ladi take ciki.
Babu ɓata lokaci, iyayenta suka tara jama’ar ƙauye, suka ɗauki makamai suka nufi bayan gari domin ceton Ladi. Bayan sun isa, suka kai wa Dodo hari, suka kashe shi. Bayan haka, suka dawo gida da Ladi cikin farin ciki da godiya.
Daga wannan rana, Ladi ta daina fita daga gida ba tare da izinin iyayenta ba, kuma ta zama mai biyayya ga magabata.
Darussa Daga Labarin
1. Rashin bin gargaɗin iyaye da magabata yana jefa mutum cikin haɗari.
2. Zaman lafiya da haɗin kai tsakanin jama’a yana taimaka wa wajen magance matsalolin rayuwa cikin gaggawa.
3. Tausayi da taimakon juna suna da muhimmanci a lokacin ƙunci.