TATSUNIYA: Labarin Sarki Gizo Da Kwarkwata
- Katsina City News
- 17 Nov, 2024
- 455
Akwai wata rana a wajen da ba nisa da garin da Sarki Gizo ke mulki, wani tsoho yana aikin gona ya hango wata katuwar kwarkwata. Ya ɗaga hannu da niyyar murƙushe ta, sai kwarkwatar ta ce:
“Kada ka kashe ni! Zan yi maka tsaro a gonarka. Kada ka kashe ni!”
Tsoho ya yi mamaki, sai ya tambaye ta:
“Idan na bar ki, me za ki yi mini?”
Kwarkwatar ta amsa:
“Ka bar ni kawai a cikin gonarka, za ka ga abin da zan yi.”
Tsohon ya ƙyale ta, amma sai ya fake cikin gonar yana kallonta. Ba da daɗewa ba, sai ga fadawan Sarki Gizo sun shigo gonar domin su yi sata. Suna shirin yanke harawar wake sai kwarkwatar ta fara waka:
> “Caca bille, caca bille,
> Burabusko bille,
> Fadawan Sarki Gizo,
> Sun zo satar harawar wake,
> Su kai wa dokin Sarki.”
Wakar ta sa fadawan suka fara rawa ba tare da sun iya ci gaba da aikinsu ba. Sarki Gizo ya lura da shiru, sai ya aika dogarawansa — Kiyashi, Yankyaso, da Fara — su bincika abin da ke faruwa. Da suka isa gonar, fadawan suka ce:
“Ku taba waken nan ku gani.”
Dogarawan sun taɓa waken, kuma nan da nan kwarkwatar ta shiga rera sabuwar wakarta:
> “Caca bille, caca bille,
> Burabusko bille,
> Fadawa sun zo,
> Dogarawa sun zo,
> Satar harawar wake,
> Su kai wa dawakin Sarki.”
Dogarawan suka fara rawa kamar fadawa. Da shiru ya yi yawa, sai Sarki Gizo ya turo manyan baradensa irin su Kudan Zuma, Kunama, Macizai, da Kwarkwasa. Suna zuwa suka yi tsawa ga fadawa da dogarawa:
“Kun raina Sarki ne? An turo ku yi aiki amma kun tsaya shirme!”
Fadawan da dogarawan suka ce:
“Ku taɓa waken nan ku gani.”
Baradensu suka taɓa waken, sai kwarkwatar ta sake waka:
> “Caca bille, caca bille,
> Burabusko bille,
> Fadawa sun zo,
> Dogarawa sun zo,
> Sojoji sun zo,
> Garin satar harawar wake,
> Su kai wa dawakin Sarki.”
Baradensu ma suka kama rawa. Da Sarki Gizo ya ga babu wanda ya dawo fada, sai ya fusata ya je gonar da kansa. Yana zuwa sai ya ga kowa na ta rawa. Da aka shaida masa abin da ke faruwa, sai aka ce:
“Ranka ya daɗe, ka taɓa waken nan ka gani.”
Sarki ya taɓa waken, kuma nan da nan kwarkwatar ta fara rera wakarta. Duk da haka, Sarki Gizo bai yi rawa ba saboda dabara da ƙarfinsa sun fi na kwarkwatar. Sai ya ce:
“Wace gonar ce wannan?”
Tsohon ya fito daga mafakarsa ya ce:
“Ranka ya daɗe, gonata ce.”
Sarki Gizo ya tambaye shi me ya yi wa gonar da ta sa hakan ke faruwa. Tsoho ya ba shi labarin kwarkwatar da yadda ta yi tsaron gonar. Sarki ya nemi a ba shi kwarkwatar, kuma ya roƙe ta ta saki fadawansa da dogarawansa. Kwarkwatar ta amince, suka daina rawar, sannan tsoho ya ba wa Sarki kwarkwatar kyauta.
Tun daga wannan lokaci, Sarki Gizo ya kasance yana jin daɗi tare da kwarkwatar, yana sa ta rera masa wakoki a lokacin farin ciki. Duk sanda yake cikin raha, sai ya tsokani fadawansa da cewa:
“Ku ne waɗanda kwarkwata ta yi wasa da ku.”
Haka rayuwar mulkin Sarki Gizo ta ci gaba da tafiya cikin farin ciki da raha.
Kurunkus!
Daga littafin taskar Tatsuniyoyi na Dakta Bukar Usman