Tinubu ya bada lambar girmamawar ta GCON ga Firai Ministan Indiya Narendra Modi.
- Katsina City News
- 17 Nov, 2024
- 231
Shugaba Tinubu ya bayyana bada lambar girmamawar ne yayin tattaunawar da aka yi tsakanin shugabannin Najeriya da Indiya a fadar gwamnatin Najeriyar dake Abuja a yau Lahadi.
“A yau ina mika maka, Firai Ministan Indiya, lambar girmamawar Najeriya mafi alfarma ta GCON. Hakan alama ce ta yabo da jajircewar Najeriya ga Indiya a matsayin kawa." kamar yadda aka ruwaito shugaban na fadi
Najeriya da kasar Indiya sun jaddada aniyar gina kwakkwarar alaka, inda suka sha alwashin karfafa dangantaka a muhimman fannoni irinsu bunkasa tattalin arziki da tsaro da kiwon lafiya da kuma samun wadatar abinci.
A yayin tattaunawar tasu, shugabannin 2 sun amince da samun karin hadin gwiwa a fannin yaki da ta'addanci da tsaron teku da kuma musayar bayanan sirri.