KTSIEC Za Ta Fara Tantance 'Yan Takara Mako Mai Zuwa
- Katsina City News
- 15 Nov, 2024
- 274
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Katsina (KTSIEC) za ta fara tantance 'yan takara daga ranar 20 ga Nuwamba 2024, a matsayin wani bangare na shirye-shiryen gudanar da zaɓukan kananan hukumomi da aka shirya yi ranar 15 ga Fabrairu 2025.
Tantancewar na zuwa ne bayan karewar wa’adin sayar da fom ɗin zaɓe na 006, 006A, da 007, wanda ya ƙare a ranar 14 ga Nuwamba 2024 da ƙarfe 11:59 na dare.
Za a gudanar da tantancewar daga ranar 20 zuwa 27 ga Nuwamba 2024. 'Yan takarar kujerar Shugaban Karamar Hukuma da Mataimakinsa za a tantance su a hedkwatar hukumar da ke Katsina, yayin da za a tantance 'yan takarar Kansila a ofisoshin kananan hukumomi daban-daban na jihar.
Hukumar KTSIEC ta ja hankalin jam'iyyun siyasa da suka sayi fom ɗin takara tare da 'yan takararsu su shirya tsaf don gudanar da tantancewar bisa jadawalin da aka amince da shi.
Hukumar ta kuma nanata cewa ba za a ƙara wani wa’adin ba. Sai dai 'yan takarar da jam’iyyunsu suka gabatar da sunayensu kuma suka cika dukkan sharuddan amsar fom za su samu damar shiga tantancewar.
Sa hannun:
Hon. Kwamishina, Adamu Salisu Ladan
Domin Shugaban KTSIEC