YADDA GWAMNA DAUDA LAWAL YA CANJA FASALIN HARKAR KIWON LAFIYA A ZAMFARA
- Katsina City News
- 11 Nov, 2024
- 261
Ganin yadda Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya samu harkar kiwon lafiya a jihar cikin wani hali na rashin kula, nan da nan ya sanya dokar ta-ɓaci a harkar, wanda daga hawansa mulkin jihar ya shiga yin garambawul.
Ba da ɓata lokaci ba gwamnan ya shiga gudanar da ayyukan inganta cibiyoyin lafiyar jihar, inda aka gyaggyara wasu, aka gina wasu sabbi, aka ɗaga darajar wasu, aka kuma sanya kayan aiki a duk cibiyoyin, sannan aka gina wasu manyan asibitoci a duk yankunan jihar.
Cikin shekara guda waɗannan manyan asibitoci masu fama da rashin inganci da rashin kayan aiki da rashin isassun Ma'aikata, wuraren da suka zama masu haɗari ga ɗan adam ya zauna a ciki, amma Gwamna Lawal ya samar da kayan aiki na zamani, samar da ƙwararrun Likitoci da sauran ma'aikatan lafiya, suka koma abin dogaro ga al'umma bisa inganci da ƙwarewa.