UNGUWAR SARARIN TSAKO.
- Katsina City News
- 10 Nov, 2024
- 383
Wannan wannan tana daya daga cikin UNGUWANNI Birnin Katsina. Daga Gabas ta yi iyaka da Gambarawa, daga yamma ta yi iyaka da kwanarya, daga Arewa ta yi iyaka da Chake, daga kudu tayi iyaka da Filin bugu da Sagi. UNGUWAR ta samo sunantane daga mazauna farko na UNGUWAR watau Buzayen Agades. Tsako Kalmar Buzaye ce da take nufin shugaba ko Sarki. A UNGUWAR Sararin Tsakone aka fara Sabkar da Sarkin Turawa. Shi Sarkin Turawa Jakada ne Tsakanin Sarkin Katsina da Fatake Buzaye. Babban aikin Sarkin Turawa shine sadar da hulda Tsakanin Sarki da bakin Buzaye da suka zo Katsina, Kuma Yana shiga Tsakanin huldar kasuwanci Tsakanin Buzaye da mutanen Katsina. Kuma shine Mai masaukin bakin Buzaye da tsaron dukiyar su da kula da sauran bukatunsu.
Ada can, lokacin ana kasuwanci Sahara, shi Sarkin Turawa Sarkin Agades ke zaben shi, Sai yazo Katsina Sarkin Katsina ya nada shi a matsayin Sarkin Turawa( Trade Consul). Har ya zuwa yanzu Gidan Sarkin Turawa Yana nan a UNGUWAR Sararin Tsako, cikin Birnin Katsina.
Sanaoin mutanen Unguwar Sararin Tsako, kasancewar su Buzaye sun hada da, sayar da Cuku da Dabino da Alkama da sauransu. Masu irin wannan Sanaar akwai Alhaji Ummaru Ulu da Alhaji Karoni da Ahmed na Turawa.
Sauran Yan Kasuwar Sararin Tsako sun hada da Alhaji Lawal Shidi, da Alhaji Bature Jikan Dada da Alhaji Shira, da Alhaji Amadu Dan Kahi Mai Atamfa, da Alhaji Iro kyaftin da sauransu.
Musa Gambo Kofarsoro.