Bankin Keystone Ya Yaba wa Gwamna Lawal Kan Inganta Abubuwan More Rayuwa a Zamfara
- Katsina City News
- 09 Nov, 2024
- 85
Bankin Keystone ya yaba wa Gwamna Lawal bisa namijin ƙoƙarin sa wajen samar da manyan abubuwan more rayuwa ga al'ummar Jihar Zamfara.
Manajan Daraktan Bankin, Hassan Imam, tare da wasu manyan jami’an gudanarwar bankin ne suka kai ziyarar ban girma ga gwamnan ranar Asabar a gidan gwamnati da ke Gusau.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an bayyana cewa bankin na gyaran makarantar firamare ta Sarkin Kudu da kuma makarantar sakandare ta Sambo, duk a babban birnin jihar, a matsayin wani ɓangare na kyautata wa al'ummar da ake kira 'Corporate Social Responsibility' (CSR).
Yayin da yake jawabi ga shugabannin bankin, Gwamna Lawal ya yaba da ƙoƙarin Keystone tare da jajircewarsu wajen tabbatar da cewa jihar Zamfara ta zama muhalli mai kyau ga kowane ɗan kasuwa.
“Sanin kowa ne cewa mun gaji tsarin da ba ya aiki sosai a jihar Zamfara. Duk da haka, wannan ba hujja ba ce don kasa yin aiki yadda ya kamata. A maimakon haka, mun mai da hankali kan gano hanyoyin ci gaba da suka fi dacewa da jihar, kuma wannan shi ne abin da muke tsaye a kai.
“Ilimi yana da matuƙar muhimmanci ga duk abin da muke yi a rayuwar mu. Ya zama ƙashin bayan kowace ingantacciyar al'umma. A gwamnatina, ilimi shi ne abu na biyu bayan tsaro.
“Ina godiya da wannan karimcin. Kamar yadda na ambata, wannan aiki zai shiga tarihi a matsayin shaida ga rawar da bankin ku ke takawa a tarihin nasararmu.
“In Sha Allahu, Zamfara za ta ƙara ƙaimi da jajircewa wajen ganin mun yi gogayya da sauran jihohin Nijeriya ta kowanne fanni.
“Ina fatan ganin an ƙaddamar da waɗannan makarantu nan ba da jimawa ba bayan kammala aikin su. Na gode ƙwarai da wannan karamci.
A jawabinsa, Manajan Daraktan Bankin Keystone, Hassan Imam, ya bayyana cewa, hukumar gudanarwar bankin ta tattauna batun shiga tsakani kafin yanke shawarar mayar da hankali kan gyara da kuma inganta makarantu a matsayin wani ɓangare na Kyautata Wa Al'umma.
“Nasarar da wannan gwamnati ta samu a cikin watanni 17 kacal ya zarce abin da magabatan ta suka cimma a cikin sama da shekaru 20. Gwamnatin Dauda ta yi fice a fannin ilimi, lafiya, da abubuwan more rayuwa. Bani da isasshen lokacin da zan lissafa duk abin da ta yi wa jihar Zamfara, amma duk wanda ya ziyarci jihar zai ga yadda aka gudanar da ayyukan titi na biliyoyin daloli.
“Mun zo nan ne domin mu ba ku goyon baya, saboda mun fahimci kwazon ku, bayan tattaunawa da dama, mun yanke shawarar mayar da hankali kan ilimi. Muna gudanar da cikakken gyare-gyare a Makarantar Firamare ta Sarkin Kudu da Makarantar Sakandare ta Sambo, a babban birnin jihar.
"A halin yanzu, 'yan kwangilar sun riga sun isa wurin, kuma aiki ya kankama," in ji shi.