Majalisar Zartaswa ta Jihar Katsina ta Amince da Bayar da Kwangilar Gyara Hanyar Da ta Tashi Daga Shargalle, Dutsi, Zuwa Ƙaramar Hukumar Ingawa
- Katsina City News
- 07 Nov, 2024
- 88
A ranar Laraba 6 ga watan Satumba 2024, Majalisar zartaswa ta jihar Katsina ƙarƙashin jagoranci Gwamnan jihar Malam Dikko Umaru Radda PhD, CON, ta amince da bada kwangilar gyaran hanyar da ma wasu muhimman ayyukan raya ƙasa a zaman majalisar karo na sha ɗaya.
Da yake sheda ma manema labarai kwamishinan ayyuka na jihar Engr. Sani Magaji Ingawa, yace" majalisar ta amince da gyaran hanyar mai tsawon kilo mita 39 akan kuɗi sama da Naira Biliyan 13.8,
Kwamishinan ya bayyana wannan shine aiki na farko da za'ayi ma hanyar tun bayan da marigayi Umaru Musa Yar'adua, ya yita shekeru Ashirin da suka gabata, ya bayyana za'a kammala aikin cikin watanni sha huɗu.
Ya ƙara da cewa" majalisar ta amince da ƙarasa wani tsohon ginin ɗakin karatu da aka fara ba'a ƙarasa ba shekaru da dama da suka gabata akan kuɗi Naira Miliyan 279, wanda za'a mai da shi ma'aikatar kasafin kuɗi da tsare-tsare ta jiha.
Ita ma Kwamishinar ilimi ta jiha Haj. Zainab Musa Musawa, tace" majalisar zartaswa ta amince da mayar da Makarantar Sakandire ta fasahar Ƙirƙira da ke Funtua (GTC) zuwa sabuwar jami'ar gwamnatin tarayya da za'a gina a garin na Funtua.
Bugu da kari Kwamishiniyar ta kara da cewa" majalisar ta amince da ƙirƙiro sabuwar dokar hukunta duk wanda aka kama ya lalata kaddarorin Gwamnati ko ɗaukar kayan makarantu a faɗin jihar Katsina.
Haka zalika majalisar ta amince da siyo awaki domin a raba ma mata a faɗin mazaɓu 361 na jihar nan domin haɓɓaka tattalin arziki, inganta kiwo da kuma rage zaman banza a jihar Katsina kamar yanda mai baiwa gwamnan shawara akan kiwo da noman rani Hon. Yusuf Suleman Jibia ya sheda.
Hon. Bishir Gambo Saulawa, Kwamishinan ruwa na jiha ya sheda majalisar ta amince da kashe Naira Biliyan Ashirin domin samar da ingantaccen ruwan sha ga al'ummar kananan hukumomin Kafur, Funtua, Ƙankara, Charanchi, Batagarawa, Dutsin-ma, Baure, da kuma Katsina.
Za'a samar da ruwan ne haɗin guiwa da shirin samar da ruwan sha na bankin duniya (SURWASH) wanda gwamnatin jihar Katsina zata bayar da Biliyan biyar a cikin kuɗin, ya baiyana zasu faɗi garuruwan da aikin ruwan zai shafa a cikin ƙananan hukumomin.
Kwamishinan Kuɗi Hon. Bishir Tanimu Gambo, ya sheda cewa" majalisar ta amince da kasafin kuɗin na shekarar 2025 wanda za'a miƙa ma majalisar dokokin jihar domin yin duba akai.
Abubakar Shafi'i
07th November, 2024