Gwamnatin Katsina Ta Fara Rage Albashi Ga Malaman da Ba Sa Zuwa Aiki
- Katsina City News
- 06 Nov, 2024
- 1512
Gwamnatin Jihar Katsina ta bullo da sabon tsari don magance matsalar kin zuwa aiki daga malamai a makarantu na gwamnati.
Hukumar Ilimin Bai ɗaya ta Jihar (SUBEB) ta sanar da cewa za a rage kashi ɗaya cikin ɗari (0.25%) na albashin duk wani malami da ya yi watsi da aikin sa har tsawon kwanaki 10 ko fiye a cikin wata guda.
Shugaban SUBEB na jihar, Kabir Magaji Gafia, ne ya bayyana wannan sabuwar doka bayan ganawar da ya yi da Sakatarorin Ilimi na kananan hukumomi 34 na jihar.
“Muna sanar da cewa daga yanzu duk wani malami da ya yi watsi da aikin sa har tsawon kwanaki 10 ko fiye a wata, za a rage masa kashi ɗaya cikin ɗari na albashinsa,” in ji Gafia.
Ya ƙara da cewa an fara aiwatar da wannan tsari a wasu kananan hukumomi kamar Mashi da Batsari, inda aka rage albashin wasu malamai bisa ga wannan doka.
Gafia ya bayyana cewa za a aiwatar da wannan tsari a dukkan kananan hukumomin jihar guda 34, tare da jan hankalin malamai da su mai da hankali ga aikinsu domin gujewa hukuncin rage albashi.
A cewar sanarwar, dokar ta riga ta fara aiki a wasu kananan hukumomi. Sai dai wasu malamai a karamar hukumar Batsari sun koka kan cewa hukumar SUBEB ba ta yi cikakken bincike don tantance hakikanin malaman da ba sa zuwa makaranta ba, amma duk da haka ta rage musu albashi fiye da adadin da aka sanar. A wata hira da Jaridar Katsina Times, wasu malaman sun bayyana cewa an cire musu albashi fiye da naira dubu ashirin, wasu kuma dubu goma sha biyar ko sha takwas.
"Wata rana daga Katsina nake zuwa Batsari koyarwa, kuma bana fashi, sai dai wani lokaci ina makara saboda matsalar mota. Amma duk da haka, aka ce sun duba, kuma a dalilin haka aka cire min kudin albashi," in ji wata malama a makarantar Batsari.
Wani malami da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa ba dukkan makarantun Batsari ake bude su ba saboda matsalar 'yan bindiga. Suma masu zagayen ganin makarantun ba sa iya shiga duk wuraren, amma duk da haka suna ikirarin cewa ana koyarwa don karkatar da kudaden ciyarwa na dalibai.
Jaridar Katsina Times ta tattauna da Sakataren Ilimi na ƙaramar hukumar Batsari, wanda ya tabbatar da cewa sun ziyarci makarantun Batsari, kuma duk wani malamin da aka rage masa albashi an tabbatar da rashin halartarsa ne ta hanyar rijistar zuwa makaranta.