MATSALAR WUTAR LANTARKI: Zamu Maka Gwamnatin Nijeriya Kotu - Imrana Jino
- Katsina City News
- 29 Oct, 2024
- 374
Zaharaddeen Ishaq Abubakar (Katsina Times)
A wani taron manema labarai da ya gudanar a ofishinsa, tsohon dan takarar gwamna na jihar Katsina a jam’iyyar PRP, Imrana Ja’afar Jino, ya bayyana shirin sa na maka gwamnatin Nijeriya da hukumomin wutar lantarki Kotu.
Haka kuma Jino yi kakkausan suka ga yadda ake gudanar da shugabanci da kuma mummunar matsalar rashin wutar lantarki da ake fuskanta a yankin arewacin Najeriya. A jawabinsa, Jino ya bukaci a dauki matakan gaggawa tare da biyan diyya ga mutanen da rashin wutar lantarkin ya shafa.
Da yake magana a matsayin wanda ya kafa kungiyar Jino Support Foundation, Jino ya bayyana cewa rashin wutar lantarki a yankin arewa ya jawo mummunan asara ga kasuwanci da rayuwar al’umma. Ya bayyana matsalar a matsayin "abin takaici a karni na ashirin da daya." Ya bukaci hukumomin TCN da kamfanonin rarraba wutar lantarki da su dauki mataki don tabbatar da ingantacciyar wuta. “Muna bukatar daina jin kukan rashin wuta kawai; mutanen mu sun sha wahala sosai,” inji shi.
Jino ya sanar da shirin kafa wata tawagar da za ta tattara bayanai kan asarar da al’ummar yankin suka yi saboda rashin wuta, inda ya bukaci gwamnati da ta biya diyya ga duk wanda asarar ta shafa. "Wannan wahalar da mutanen mu ke sha dole a dauke ta da muhimmanci," inji Jino.
Har ila yau, Jino ya bayyana rashin gamsuwarsa kan yadda ake gudanar da al’amuran kudin jihar Katsina, yana zargin akwai rashin gaskiya a bangaren shugabanci da rashin bin ka’idojin kasafin kudi. Ya ce yana da shirin bin diddigin kudaden kasafin jihar domin tabbatar da cewa an kashe su yadda ya dace. “Za mu fito fili mu fallasa yadda aka kashe kasafin kudin jihar Katsina." inji Jino, yana mai kira ga al’ummar jihar su san hakkokinsu kuma su nemi bayanai.
Jino ya bukaci ‘yan arewa musamman a kafafen sada zumunta da su hada kai wajen yada wannan kira, tare da rokon al’umma su zabi shugabannin da za su magance wadannan matsaloli masu ban takaici.