Gwamna Lawal Ya Ba Da Kyautar Mota Ga Ƙungiyar Tsaffin Manyan Sakatarorin Da Suka Yi Ritaya A Zamfara
- Katsina City News
- 18 Oct, 2024
- 171
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bai wa Ƙungiyar Tsaffin Mayan Sakatarorin jihar Zamfara mota ƙirar Bas mai ɗaukar mutane 18.
Gwamnan ya miƙa bas ɗin ne ga shugabannin ƙungiyar a ranar Laraba a gidan gwamnati da ke Gusau.
A taron shekarar da ta gabata, Gwamna Lawal ya yi alƙawarin samar da motar bas ga ƙungiyar domin sauƙaƙa zirga-zirga a lokacin gudanar da ayyukanta.
“Alhamdulillah, yau na cika muku wannan alƙawari. Ina roƙonku da ku yi amfani da motar a cikin ayyukanku na yau da kullum.
“Gwamnatina za ta ci gaba da ba ku dukkan goyon bayan da suka dace. Kun yi wa Jihar Zamfara hidima sosai, kuma yanzu lokaci ya yi da gwamnati za ta tallafa wa ƙungiyar ku.”
Da yake karbar bas ɗin a madadin ƙungiyar, tsohon shugaban ma’aikata na jihar Zamfara, Alhaji Bello Karakkai, ya nuna jin daɗinsa ga gwamnan bisa yadda ya saba cika alƙawuran da ya ɗauka.
"Muna alfahari da wannan karimcin kuma za mu tabbatar da cewa mun yi muhimman abubuwa ga ƙungiyarmu.
“Wannan shi ne karon farko da gwamna ya saurare mu tun da aka kafa jihar. Muna farin ciki matuƙa. Allah Ya saka da alheri.”