Tatsuniya; Labarin Kurege da Biri

top-news

Kurege da Biri sun ga wata yarinya, kowannensu yana son ya aureta. Kowannensu ya aikata neman izinin auren ta daga iyayenta. Sai iyayen yarinyar suka ce duk wanda yake so ya auri ‘yarsu sai ya kawo fatun namun daji.

Da Kurege ya ji wannan sharaɗi, sai ya tafi wurin Kaza, ya ce da ita: "Ina gayyatar ki ki taimaka mini aiki a gonata gobe."

Kaza ta amsa da cewa: "Zan zo, amma ka tabbatar kada ka gaya wa Kyanwa."

Kurege ya ce da ita: "Tabbas, ba zan gaya mata ba."

Bayan haka, Kurege ya nufi gidan Mage, ya ce da ita: "Ina son ki taimaka mini a gona gobe."

Mage ta ce: "Zan taimaka, amma kada ka gaya wa Kare. Ka san idan ya gan ni a gona zai cinye ni."

Kurege ya ce: "Na sani, wa zai gayyaci Kare kuwa?"

Daga nan, Kurege ya tafi gidan Kare, ya ce da shi: "Ina so ka taimaka mini aiki a gona gobe."

Da gari ya waye, Kurege da Kaza suka isa gona tun da sassafe, suna cikin aiki sai ga Mage ta iso. Sai Kurege ya ce da Kaza: "Maza ki buya a cikin ciyawa."

Mage ta iso kusa da Kurege, sai ta ce: "Kai da wa kake magana?"

Kurege ya ce: "Ni da Kaza nake magana, ga ta can tana cikin ciyawa. Idan kin kashe ta, ki bar mini fatar."

Mage nan take ta gano inda Kaza take, ta kashe ta ta cinye naman ta, ta bar wa Kurege fatar.

Bayan nan, Kurege da Mage suka ci gaba da aiki. Jim kadan sai ga Kare ya iso yana haki, yana cewa yara sun bi shi suna son su kashe shi. Bayan Kurege ya yi masa barka da zuwa, sai Kare ya tambaye shi: "Kai da wa kake wannan aiki?"

Kurege ya ce da shi: "Ni da Mage nake aiki, ga ta can tana aiki. Idan ka kashe ta, ka bar mini fatar."

Kare ya yi godiya, ya tafi ya kashe Mage, ya bar wa Kurege fatar.

Kare ya ce da Kurege: "Ka tabbata ba ka gaya wa Kura ba, idan ka gaya mata ba zan zo ba."

Kurege ya tabbatar masa cewa ba zai gaya wa Kura ba. Amma daga nan sai ya je gidan Kura. Da suka gaisa, sai ya ce da ita: "Ina gayyatar ki ki taimaka mini aiki a gona gobe."

Kura ta ce: "Ba zan sami lokacin ba, zan je cin wani mushe da na gani."

Kurege ya roƙeta sosai, har sai da ta amince da zuwa. Ta ce: "Zan zo, amma ka tabbata ba ka gaya wa Damisa ba."

Kurege ya ce: "Ba komai, ba zan gaya mata ba."

Daga nan, sai Kurege ya tafi gidan Damisa. Ya ce da ita: "Ina roƙon ki ki taimaka mini aiki a gona gobe."

Damisa ta ce: "Zan taimaka, amma ina son in san ko wa ka gayyata?" Kurege ya ce: "Kura ce kawai."

Damisa ta ce: "Lallai zan zo."

A gobe da asuba, Kare da Kurege suna aiki a gonar, sai ga Kura ta iso. Kurege ya ce da ita: "Kawata, ai Kare yana barci a can. Idan kin kashe shi, ki bar mini fatar."

Nan take, Kura ta kashe Kare, ta bar wa Kurege fatar.

Bayan haka, Kurege da Kura suka ci gaba da aiki. Can kuma sai ga Damisa ta iso. Kurege ya ce da Kura: "Kawata, ki buya, ga baki masu zuwa."

Kura ta buya, amma Damisa ta gano inda take, ta kashe ta ta cinye naman ta, ta bar wa Kurege fatar.

Da Damisa ta tafi, Kurege ya tattara fatun da ya tara, yana cikin farin ciki. A lokacin, Biri ya samu labarin abin da Kurege ya aikata, ya kuma ji yana cewa shi ne zai auri yarinyar.

Biri sai ya yi dabara ya zuba gyada a hanyar da Kurege zai bi don kai fatun. Da Kurege ya kama hanya, sai ya fara ganin gyada a warwatse. Ya tsaya yana ci yana cewa: "Yau dadi goma! Na sami fatu, kuma ga gyada."

Biri ya yi tsai da shi wajen cin gyada, yayin da Kurege ya manta da fatun. Biri ya yi sauri ya dauki fatun ya kai wa iyayen yarinyar, suka ba shi auren ta.

Bayan Kurege ya gama cin gyada, sai ya waiwayo don daukar fatun, amma sai ya tarar babu komai. Ya fahimci Biri ne ya dauki fatun. Daga nan ya ce bari in kai musu sauran gyadar da ragowar abubuwan, ko za su amince da ni.

Da ya isa wurin iyayen yarinyar, suka ce masa Biri ya riga ya kawo fatun, kuma an daura masa aure da yarinyar.

Kurege ya ba su ragowar gyadar da ya kawo, sannan ya ce: "Ku yi amfani da ita, ku kuma soya ku ci. Ga igiyar da za ku yi amfani da ita don daurin aurenku."

Bayan haka, Kurege ya je gidan Biri don ya taya shi murnar aure, amma ya tarar da Biri yana barci. A lokacin, sai Kurege ya sa masa wani magani a bakinsa, wanda ya haifar da mutuwarsa.

Bayan ya tabbatar da mutuwar Biri, sai Kurege ya dauki wani garin dawa daga gidan, ya sanya a bakinsa don a ce garin ya yi masa yawa ya kashe shi. Amaryar Biri ta shigo ta ga mijinta ya mutu, sai ta fara kuka.

Kurege ya ce da ita: "Akwai wani dodo a daji, yana iya gaya mana abin da ya kashe miki miji."

Amaryar Biri ta bi shi zuwa cikin daji. Bayan sun isa dajin, sai Kurege ya zana jikinsa da gawayi, ya canza kamanninsa ya zama kamar dodo, sai ya ce: "Ke wacece, me ya kawo ki nan?"

Amaryar Biri ta ce: "Mijina ya mutu, ina son sanin wanda ya kashe shi, kuma ina son sanin wanda zan aura."

Kurege cikin shigar dodo ya ce: "Ai Kurege shi ne abokin Biri, kuma kanensa ne. Ko shi za ki aura?"

Ta ce: "Haka ne, zan aura shi?"

Dodo ya kada kai ya ce: "Eh, za ki auri Kurege."

Bayan haka, sai ta koma gida. Kurege ya je wurin da ya yi wanka ya wanke jikinsa, sannan ya dawo gidan yana kuka.

Amaryar Biri ta ce da shi: "Me yasa kake kuka?"

Sai ya ce: "Na tuna da dan'uwana da abokina."

Amaryar ta ce: "Dodo ya ce kai zan aura, ka daina kuka, mu tafi gidan iyayena a daura mana aure."

Aka daura wa Kurege aure da amaryar Biri, suka zauna cikin farin ciki.

Abubuwan da Labarin Yake Koyarwa:

1. Zamba da cin amana ba su kaiwa ga nasara.
2. Dole a yi abu da hankali da hikima don samun nasara.
3. Karya tana fure, amma ba ta 'ya'ya.
4. Matar mutum ita ce kabarinsa.