Hukumar Shige da Fice Ta Yi Wa Jami'anta Karin girma A Jihar Katsina
- Katsina City News
- 10 Oct, 2024
- 161
Muhammad Aliy Hafiziy, Katsina Times
A wani gagarumin taron da aka gudanar a Hedikwatar Hukumar Shige da Fice ta Jihar Katsina dake kan titin Dutsinma, Kwamptroller Mohammed Adamu Mahmoud, PCC, FCILRM, CNA, ya yi wa sabbin jami’an da aka kara musu matsayi ado da lambar yabo a matsayin sabbin shugabanni.
Taron, wanda ya kasance wani babban ci gaba a tarihin hukumar, ya samu halartar manyan baki daga hukumomin tsaro daban-daban, inda aka yaba wa jami’an da aka kara musu girma bisa sadaukarwarsu da kuma aikinsu na tsawon lokaci.
A cikin jawabin da ya gabatar, Kwamptroller Mahmoud ya taya sabbin jami’an murna bisa karin girman da aka yi musu, inda ya jinjinawa shugabar Hukumar Shige da Fice ta Kasa, Kemi Nanna Nandap, PCC, FSM, bisa kyakkyawan jagorancin da ta ke yi wajen inganta jin dadin jami’an hukumar.
Ya jaddada cewa karin girma ba wai kawai yana nufin samun yabo ba ne, harma yana kuma nuni da kara nauyin da ya hau kansu. Ya kuma bukace su da su tunkari sabbin kalubale da tsayin daka da jajircewa.
"Karin girman da kuka samu hujja ce ta kokarinku a baya, amma yanzu lokaci ne na yin abinda ya fi na baya. Jagoranci yana nufin jan ra'ayin wasu, kuma sabbin mukamanku suna bukatar jajircewa da kwarewa," inji Mahmoud, yayin da ya kuma yi kira ga wadanda ba su samu karin matsayi ba da su kasance masu hakuri da sadaukarwa.
Daga cikin manyan baki da suka halarci taron sun hada da Kwamptroller na Hukumar Gyaran Hali, wanda yanzu aka kara masa girma zuwa Mataimakin Kwamptroller Janar, da kuma wakilan Hukumar Kula da Gobara ta Kasa da Hukumar Tsaro ta Farar Hula.
Iyalan jami'an da aka karama girma, abokai, da masoya sun cika wajen cikin farin ciki, inda suka taya su murna bisa wannan nasara da suka samu.
A madadin sabbin jami’an da aka kara wa matsayi, DCI Sulaimanu Yusuf ya bayyana godiyarsa ga Allah Madaukakin Sarki, da Kwamptroller Janar, da kuma Hukumar ta Jihar Katsina bisa goyon bayansu marar yankewa.
Ya bayyana karin girman da aka yi musu a matsayin babban kalubale na kara jajircewa, inda ya bukaci abokan aikinsa da su ci gaba da yin aiki da gaskiya da biyayya ga ka'idojin aikin su.
Taron ya zama sabon babi ga Hukumar Shige da Fice ta Jihar Katsina, yayin da take kara karfin jami'anta da sabon jagoranci da kuma himma wajen aiwatar da ayyuka.