Gwamna Radda Bai Nemi Soke Kwangilar Gyaran Titin Mararrabar Kankara ba – Inji Dr. Zango
- Katsina City News
- 09 Oct, 2024
- 220
Gwamna Radda Bai Nemi Soke Kwangilar Gyaran Titin Mararrabar Kankara ba – Inji Dr. Zango
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Kwamishinan Ma’aikatar Yada Labarai ta Jihar Katsina, Dr. Bala Salisu Zango, ya karyata rahoton wasu kafafen yada labarai, wadanda suka ce Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya nemi soke kwangilar gyaran titin Mararrabar Kankara, Dutsinma zuwa Katsina.
A cewar Dr. Zango, wannan rahoto ba gaskiya ba ne, domin abin da Gwamna Radda ya nema shi ne a maida kwangilar ga wani kamfani mai kwarewa da gogewa don tabbatar da ingancin aikin. Wannan bukatar ta Gwamnan tana nuna jajircewarsa wajen samar da kayayyakin more rayuwa da za su amfani jama’a tare da dorewa na dogon lokaci.
Kwamishinan ya bayyana cewa, Gwamnan yana kokarin ganin an yi aikin da zai kawo dorewa da inganci ga titin, ta yadda zai zama amintacce ga masu amfani da shi. Ya ce wannan gyara yana da muhimmanci domin a guji yada labarai marasa tushe da za su jefa jama’a cikin rudani.
A ranar Lahadi, 5 ga Oktoba, 2024, a wajen raba tallafin shinkafar Gwamnatin Tarayya, Mataimakin Shugaban Kasa a harkokin siyasa, Hon. Ibrahim Kabir Masari, ya bayyana cewa kwangilar gyaran titin Mararrabar Kankara, Dutsinma zuwa Katsina an bai wa wani ɗan kwangila mara kwarewa. Saboda haka, Gwamna Radda ya nemi a sauya kwangilar ga kamfani mai kwarewa don tabbatar da an yi aikin yadda ya kamata.
Dr. Zango ya nuna takaicinsa kan yadda kafofin suka kasa yin cikakken bincike kafin wallafa labarin, inda suka gaza samun bayanin daga bangaren gwamnatin jihar. Ya kuma yi kira ga 'yan jarida su rika yin aikin su bisa adalci da tabbatar da gaskiya a cikin labaransu.