Gwamnatin Zamfara Ta Biya Bashin Sama Da Naira Biliyan 9 Ga Tsoffin Ma’aikata
- Katsina City News
- 05 Oct, 2024
- 348
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kammala biyan bashin haƙƙoƙin tsoffin ma’aikatan da suka bar aiki tun daga shekarar 2011, wanda ya kama jimillar Naira 9,357,743,281.35. Wannan biyan bashin ya fara tun a watan Faburairun da ya gabata, bayan gwamnan ya amince da biyan tsoffin ma’aikatan haƙƙoƙin su.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar yau a Gusau, ya bayyana cewa gwamnatin Zamfara ta riga ta kammala biyan tsoffin ma’aikata na jiha da ƙananan hukumomi. Ya ce jimillar Naira 4,860,613,699.22 ta riga ta biya ga rukuni-rukuni 9 na tsoffin ma’aikatan jiha, yayin da tsoffin ma’aikatan ƙananan hukumomi suka samu Naira 4,497,129,582.13.
Idris ya bayyana cewa gwamna Lawal ya jajirce wajen ganin an biya haƙƙoƙin tsoffin ma’aikatan da suka shafe shekaru suna jiran biyan su. A watan Faburairu, gwamnan ya ƙaddamar da wani kwamitin da zai tantance tsoffin ma’aikatan da ba a biya haƙƙoƙin su ba tun daga shekarar 2011, tare da tabbatar da cewa an biya su haƙƙoƙin su cikin gaggawa.
Ya zuwa yanzu, daga cikin tsoffin ma’aikatan jiha 3,880 da aka tantance, mutum 2,666 sun karɓi haƙƙoƙin su, wanda ya kai Naira 4,860,613,699.22. Wadannan ma’aikata sun bar aiki daga shekarar 2015 zuwa 2024. Haka kuma, daga cikin tsoffin ma’aikatan ƙananan hukumomi da malaman firamare 4,804 da aka tantance, mutum 3,840 ne suka karɓi haƙƙoƙin su a cikin rukuni 9, wanda ya kai ga jimillar Naira 4,497,129,582.13.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa haƙƙoƙin barin aiki na tsoffin ma’aikatan ƙananan hukumomi da malaman firamare ya kai jimillar Naira 5,688,230,607.20, daga ciki an biya Naira 4,497,129,582.13. Waɗanda suka amfana sun bar aiki ne tsakanin shekarar 2011 zuwa 2021.
A taƙaice, gwamnatin Zamfara ta kammala biyan haƙƙoƙin tsoffin ma’aikatan jiha da na ƙananan hukumomi wanda ya kama jimillar Naira 9,357,743,281.35 daga cikin bashin Naira 13,784,179,513.80 da tsoffin ma’aikatan suke bi. Daga cikin tsoffin ma’aikatan da aka tantance su 8,684, mutum 6,506 ne aka biya haƙƙoƙin su. Waɗannan ma’aikata sun bar aiki ne tsakanin shekarun 2011 zuwa 2024.