Gamayyar Kungiyoyin Agaji da Hisbah a Bindawa Sun Bayar da Goyon Baya ga Hukumar Hisbah ta Katsina

top-news

A ranar Talata, 17 ga watan Satumba, gamayyar kungiyoyin agaji da kungiyar Hisbah na Ƙaramar Hukumar Bindawa sun ziyarci Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina domin jaddada goyon bayansu ga jagorancin babban kwamandan hukumar, Sheikh Dakta Abu Ammar.

Ziyarar da ta gudana a karkashin jagorancin Imam Sabi’u Bindawa, ta bayyana nasarorin ayyukan hadin gwiwa da kungiyoyin agaji ke gudanarwa tare da Hukumar Hisbah. Haka kuma, sun jinjina wa shugabancin Dakta Abu Ammar bisa namijin kokarinsa na tabbatar da kyawawan manufofi a jihar.

A nasa bangaren, babban kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, Dakta Aminu Usman, ya nuna farin cikinsa bisa wannan ziyara. Ya kuma yi kira da a ci gaba da hada kai da kungiyoyin agaji domin cigaba da yaki da duk wani aikin da ke saba wa al'ada da tarbiyya a ƙaramar hukumar Bindawa da ma jihar Katsina baki ɗaya.

Haka zalika, Dakta Aminu Usman ya bayar da shawarwari kan yadda za a kara inganta wannan haɗin gwiwa tsakanin Hisbah da kungiyoyin agaji domin samun nasarorin da za su amfani al’umma wajen kare mutunci da tarbiyya.
NNPC Advert