Babbar Kasuwar Katsina Zata Sake Kamawa Da Wuta, Cewar 'Yan Kasuwa
- Katsina City News
- 14 Sep, 2024
- 527
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times, 14 Satumba 2024
“Babbar Kasuwar Katsina wato Fadima Baika Central Market, zata sake yin wata mummunar gobara, kuma wannan zai fi muni fiye da wacce ta faru shekaru uku da suka gabata,” inji wasu daga cikin ‘yan kasuwar da suka yi hira da Katsina Times. Sun yi wannan furuci ne bayan zarge-zargen zalunci da suka yi kan yadda aka raba shagunan kasuwar, wanda suka ce an tauye hakkinsu, sunce ba ba za su bar shagunan su ba sai dai in an kashe su a cire gawarsu daga ciki.
Ismail Tijjani, Bishir Mamman Remawa, Danzaki Ikon Allah, da Malam Ahamed Rufa’i su ne suka wakilci fiye da mutum hamsin da suka bayyana cewa an zalunce su ta hanyar amshe shagunan su a cikin Babbar Kasuwar ta Katsina tare da sauya masu wasu marasa Daraja.
“A lokacin gwamnatin da ta gabata, mun yi korafi ga Gwamna Aminu Bello Masari cewa a barmu mu gina shagunanmu da kanmu don gudun irin wannan matsala. Gwamna ya saurari kokenmu, ya ce gwamnati za ta gina shagunan, sannan za a dawo ma kowa shagon sa, kuma haka aka yi. Yau shekarar mu daya da rabi muna cikin sabbin shagunan, amma don son zuciya da rashin adalci, sai kawai muka ji ance an canza mana shago daga wajen da muka saba zuwa cikin lungun kasuwa," inji Bishir Remawa.
Bishir ya ce fiye da shekaru 22 yana kasuwanci a wannan shago, ya dauki ma’aikata fiye da biyar a karkashinsa tun lokacin da babu kowa a kasuwar. Amma yanzu sabon shugaban kasuwar tare da wasu da suke waje, sun aiko da takardar cewa an mayar da shagonsa cikin lungun kasuwa.
Shi ma Ismail Tijjani ya bayyana wannan abu a matsayin rashin adalci babba. Ya yi gargadin cewa idan gwamnati bata shiga cikin lamarin ba, za a samu matsala mai tsanani a tsakanin ‘yan kasuwa, kuma kasuwar Central Market za ta fuskanci mummunan rikici. Ya roki Gwamna Malam Dikko Umar Radda da ya gaggauta shiga cikin wannan lamari domin guje wa barkewar rikici.
Danzaki Ikon Allah, a nasa bangaren, ya bayyana cewa amshe masa shago tamkar daukar masa rayuwa ne. Ya yi alkawarin cewa duk wanda ya zo yunkurin kwace masa shago, zai kare kansa kamar yadda ake kare kai a yayin garkuwa da mutane. Ya yi zargin cewa akwai rashin jituwa tsakanin sabon shugaban kasuwar da tsohon shugaban, wanda ya sa ake tauye hakkokin duk wadanda suke da kyakkyawar hulda da tsohon shugaban.
‘Yan kasuwar sun kuma bayyana cewa wasu daga cikin 'Yan Kasuwar sun mutu wasu sun rasa dukiyarsu a sakamakon gobarar da ta faru a baya, amma bayan gina shagunan sai aka ba wasu masu hannu da shuni shagunan su, aka tauye wadanda suka dade suna kasuwanci a kasuwar.
Sun zargi sabon shugaban kasuwar da shirya makarkashiya don amfana da kansa, inda suka ce ya amshi kudi daga wasu mutane na waje, sannan ya fake da cewa sabuwar gwamnati ta canza tsarin rabon shagunan. A cewarsu, shagunan da darajar su ta kai miliyan goma, an kwace masu, an ba su wadanda ba su kai miliyan biyu ba.
Dangane da wannan batun, mun yi kokarin jin ta bakin shugaban kasuwar, Malam Usman Shehu Koza, amma wayarsa a kashe take, mun aika masa sakon karta kwana, har zuwa lokacin hada wannan rahoto, bai mayar da martani ba.