GWAMNA LAWAL YA BA DA SAMA DA NAIRA BILIYAN 11 DON AIKIN INGANTA ILIMIN ’YA’YA MATA A ZAMFARA
- Katsina City News
- 12 Sep, 2024
- 196
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ƙaddamar da shirin raba maƙudan kuɗaɗe ga Ƙanana da Matsakaitan Makarantu (SIGS) a ƙarƙashin shirin Samar da Ilimi da Ƙarfafa ’Ya’ya Mata (AGILE) a jihar.
A ranar Larabar da ta gabata ne gwamnan ya raba wa ’yan kwangilar da aka zaɓa a matsayin Masu Gudanar da Ayyuka na Musamman takardun fara aiki don ayyukan gyara da kuma inganta makarantu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta ce aikin na da nufin inganta dukkan makarantu a faɗin jihar.
Ya ƙara da cewa, rabon kuxin shi ne kashi na farko na tallafin inganta ƙananan makarantu (SIGS) a ƙarƙashin shirin AGILE.
Da yake gabatar da nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa an zaɓo makarantu 322 domin gudanar da aikin, wanda kuɗinsu ya kai Naira 11,736,000,000.00.
“A yau wani gagarumin ci gaba ne a cikin ƙudirinmu na cika alƙawuran yaƙin neman zaɓe na farfaɗo da harkar ilimi a Jihar Zamfara yayin da muka ƙaddamar da shirin bayar da tallafin Inganta Makarantu (SIGS) a ƙarƙashin shirin AGILE.
“Idan za ku iya tunawa cewa mun ayyana dokar ta-ɓaci a ɓangaren ilimi, kuma wannan shirin na nuni da ci gaba da shawarar da muka yanke na gyara da kuma inganta ababen more rayuwa a makarantu.
“Saboda haka, wannan taro wani muhimmin mataki ne a cikin tsarin, domin an raba wa ’yan kwangilar da aka zaɓa a matsayin Masu Gudanar da Ayyuka na Musamman takardun fara aiki don ayyukan gyara da kuma inganta makarantu.
“Wannan mataki ne mai muhimmanci wajen samar da ingantaccen yanayin samun ilimi ga yaranmu.
“A matsayinku na Masu Gudanar da Ayyuka na Musamman, rawar ku na da muhimmanci wajen tabbatar da cewa kowace naira da aka kashe ta nuna kanta a ci gaban da aka samu a makarantunmu.
Gwamna Lawal ya kuma buƙaci Masu gudanar da ayyuka na musamman ɗin da su bi tsare-tsaren inganta makarantu (SIPS) da ƙa’idoji yadda ya kamata.
“A yunƙurinmu na tabbatar da cewa aikin ya kai matsayin da ake buƙata, mun kafa wata hanya mai ƙarfi don sa ido kan aiwatarwa da kuma tabbatar da bin duk ƙa’idoji da ƙayyadaddun bayanai.
“Ina kuma kira ga tawagar sa ido kan ayyukan da kwamitin gudanarwa na makarantu (SBMC), da sauran jama’a da su kasance cikin shiri da kuma tsunduma cikin wannan aiki. Wannan yunƙurin ba wai kawai na gina makarantu da sabunta su ba ne; ya shafi zuba jari ne a makomar jihar Zamfara.”