Dan Majalisar Katsina Ya Tallafawa Marasa Karfi Don Rage Raɗaɗin Rayuwa
- Katsina City News
- 09 Sep, 2024
- 229
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times, Satumba 9, 2024
Dan Majalisar Wakilai na Karamar Hukumar Katsina, Alhaji Aliyu Abubakar Albaba, ya tallafawa marasa ƙarfi da waɗanda ruwan sama ya yi wa barna a cikin Katsina.
A ranar Litinin, dan majalisar ya kaddamar da rabon tallafin a mazabu 12 na Karamar Hukumar Katsina, inda kowace mazaba za ta samu buhunan shinkafa 80 da buhunan siminti 100, waɗanda za a ba waɗanda ruwan sama ya rusa musu gidaje.
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, wanda shi ne babban bako a wajen taron, ya yabawa wannan tallafi, inda ya bayyana cewa dan majalisar ya nemi gudanar da wannan aiki ba tare da ya bayyana ba. Gwamnan ya ce, "Ni ne na ba shi shawara da ya bayyana, saboda duk abin siyasa bayyana shi ake yi don kowa ya yi koyi." Ya kuma yi kira ga sauran masu rike da mukamai na siyasa da su yi duba ga halin da jama'a ke ciki, tare da yin abin da zai rage musu radadin rayuwa.
A cikin jawabinsa, Alhaji Aliyu Abubakar Albaba ya ce dukkan mazabu 12 na Katsina za su samu buhun siminti 100 da karamin buhun shinkafa 80. Ya ce an yi haka ne domin taimakawa al’umma wajen rage matsin rayuwa, da kuma taimakawa waɗanda ruwan sama ya shafa wajen sake gina gidajensu.
Hakazalika, ya bayyana cewa kungiyoyin masu zaman kansu, kafafen yaɗa labarai, masu buƙata ta musamman, da jam’iyyarsa ta APC suma sun amfana daga wannan tallafi.
Ya ƙara da cewa an yanke shawarar kawo kayan mazaba guda zuwa wajen kaddamarwa domin kaucewa matsalolin kwace ko hayaniya yayin kai kayan gida. Saboda haka, katin shaida zai kasance ga duk wanda ya cancanta don ya tafi ya karɓi tallafinsa a wurin da aka tanada.
An gudanar da taron kaddamarwa a filin wasa na Muhammadu Dikko da ke garin Katsina, tare da halartar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, wasu 'yan majalisa, masu rike da sarautar gargajiya, ciki har da Magajin Garin Katsina, Hakimin Zakka, da Hakimin Daddara, da sauran jiga-jigan siyasa na karamar hukumar Katsina.